✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daruruwan ‘yan Rasha na barin kasar don gudun shiga aikin soja

‘Yan kasar Rasha sama da 10,000 ne ke tsallaka wa Jojiya a kowacce rana.

Daruruwan matasa ‘yan kasar Rasha ne ke tsallakawa makwabciyar kasar Jojiya a kokarinsu na guje wa shiga aikin soja.

Jami’an shige da fice na kasar Jojiyan sun ce ‘yan kasar Rasha sama da 10,000 ne ke tsallaka kan iyakan kasar daga Rasha a kowacce rana.

Haka ma wusu hotunan jerin gwanon motoci a kan hanyar iyakar kasar da Mongolia da kuma Jojiyan sun karade dandalin sada zumunta da mahawar na ‘yan kasar da ke barin gari.

Bugu da kari, kudin tikitin jiragen sama daga Rasha zuwa kasashen waje ya yi tashin gwauron zabi, a cewar wani rahoto na Al Jazeera.

Wannan kiran shiga aikin soji don kara yawan sojojin kasar a yakin da Rashan ta ke yi da Ukaine daga shugaba Vladmir Putin, ba ta tsaya ga samari ba, su ma wadanda suka taba aikin soja shugaban ya ce su fito.

Kazalika, wadanda ma ba su taba aikin soja ba ma, shugaban ya ce su fito.

Rahotanni na cewa Rasha ta yi hasarar sojojinta da yawa a yakin da ta ke gwabzawa da Ukraine wanda hakan ya tilasta mata daukar sabbi don cike gibi.