✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministan Tsaron Ukraine Oleksii Reznikov zai yi murabus

Ya kamata mu sauya dabarun mu wajen tunkarar matsalar tsaro a cewar Shugaba Zelensky.

Ministan Tsaron Ukraine Oleksii Reznikov ya mika takardar yin murabus a ranar Litinin.

Wannan na zuwa ne yayin da a jiya Lahadi, Shugaban Kasar Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa ma’aikatar tsaron na bukatar sabbin hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen kalubalen da kasar ke fuskanta.

Sauyin shugabancin ya biyo bayan zarge-zargen cin hanci da rashawa da dama a cikin ma’aikatar tsaron kasar.

“Na mika wasikata ta murabus ga Ruslan Stefanchuk, shugaban majalisar dokokin Ukraine.

“Abin alfahari ne na yi hidima ga al’ummar Ukraine da kuma yin aiki ga sojojin kasata na tsawon watanni 22, lokacin da ya kasance mafi tsanani a tarihin Ukraine,” in ji Reznikov.

Zelensky ya ce ya yanke shawarar maye gurbin ministan tsaronsa, wanda shi ne mataki mafi girma da aka samu tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a watan Fabrairun 2022.