✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dariye ya musanta batun tsayawa takara a Zaben 2023

Ban yi duk wasu tanade-tanade ba da ake yi na tsayawa wannan takara ba.

Tsohon gwamnan Jihar Filato, Cif Joshua Chibi Dariye, ya musanta labarin da ake yadawa cewa zai tsaya takarar kujerar Sanata a karkashin jam’iyyar Labour a zaben badi.

Dariye ya musanta batun takararsa ce yayin da ya karbi tawagar gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong da ta kai masa ziyarar taya shi murnar fitowarsa daga gidan yari.

Ya ce “sam, babu gaskiya a wannan labari, domin ban sayi fom na tsayawa wannan takara ba, kuma ban yi duk wasu tanade-tanade ba da ake yi na tsayawa wannan takara ba.

Ya yi godiya ga Allah kan yadda Ya kaddara aka sake shi daga wannan dauri da aka yi masa.

Kazalika, ya mika godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamna Lalong kan yadda suka tsaya wajen ganin ya shaki iskar ’yanci.

Da yake nasa jawabin, gwamna Lalong ya bayyana cewa al’ummar Jihar Filato sun yi farin ciki da sakin tsohon gwamnan jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, a Litinin din da ta gabata ce aka saki tsohon gwamnan da wasu daga gidan yari, bayan ya shafe kusan shekara hudu a daure, sakamakon kama shi da laifin wawure kudin gwamnatin jihar fiye da naira biliyan daya.

Kasa da mako guda da sakin tsohon gwamnan, maganar sake tsayawa takararsa domin neman kujerar Sanata a mazabar Filato ta tsakiya ta fara fitowa kuma a hankali maganar sai kara karfi take yi.