✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dare Dubu Da daya (2)

Wannan bayani duk da cewa an dade ana yin ina-aka-saka da shi ya samo asali daga cikin budewar littafin tun da farko inda masu ruwayar…

Wannan bayani duk da cewa an dade ana yin ina-aka-saka da shi ya samo asali daga cikin budewar littafin tun da farko inda masu ruwayar suka yi nuni da haka, suna cewa, “ku sani, a can da, an taba yin wadansu labarai da hikayoyi wadanda ake ambatar su da Dare Dubu. Akwai cikin wadannan labarai abubuwan nishadantarwa da sababbin labarai da hadisai masu gangarowa da misalai don hankaltarwa, kamar yadda za a gani a nan.”

Ba wani abu ya sa wasu suka amince da wannan hujja da ke nuni da samuwar wani littafi mai kama da wannan ba sai ganin ko kafin a samar da littafin Alfu Laila da Larabci akwai labarin Sarki Shaharuman da wazirinsa da ‘ya’yan wazirin biyu, ‘yan mata, Shaharuzad da Dunyazad da labarin tafiye-tafiyen Sindibad, a cikin littafin Hazar Afsanah, wanda shi ne littafin farko, wanda daga baya kuma aka same su a cikin littafin Alfu Laila.

In aka koma kan batun shekara ko lokacin da aka wallafa litttafin, nan ma ra’ayi ya bambanta. Abin da aka fi yarda a kai shi ne, an wallafa littafin ne a tsakanin karni na 10 zuwa na 16, Miladiyya. An gano haka ne ta bin diddigin ginuwar wasu labarai da wakokin da ke ciki da al’adu da tadojin jama’ar da labaran ke magana kan su da wasu abubuwa da suka hada da kayan kida da yake-yake da ke ciki. Daga kunshiyar wasu wakokin aka fahimci akwai labaran zamanin jahiliyya da kuma na zamanin wasu halifofi, kamar Haruna Rashid da kuma labaran da suka wanzu daga karni na 15 zuwa na 16, da kuma kafin nan, kamar shan giya da taba duk sun auku ne kafin karni na 15.  Inda aka yi maganar bindiga da alburushi kuwa ana maganar zamanin karni na 16 da 17 ne, lokacin da Turawa suka kirkiro su, har aka samar da su ga sauran al’ummomi.

Saboda haka muna iya cewa matanin littafin Alfu Layla na Larabci shi ya fi yin tashe sosai, ya zama mashahuri matuka, ya shiga watayawa zuwa sassan duniya daban-daban, ciki kuwa har da kasar Hausa. Wannan na Larabcin ne kuma aka yi aikin sa zuwa sauran harsunan daban-daban na duniya, ciki har da Ingilishi. Matanin Alfu Laila na Ingilishi ya iso kasar Hausa daga bayan wajejen 1884, lokacin da aka wallafa shi a Turai.

Fassara Alfu-Laila zuwa harsunan Turai da wasu kasashen duniya ya faro ne daga karni na 18, inda aka sami wani wai shi Gaul ya soma wannan aiki, duk da yake ba littafin ne ya fassara bisa jimillarsa ba. Fassara ta ainihi ita ce wadda Galland ya yi tsakanin 1704-1717 da harshen Faransanci, sai kuma wadda ban Hommer ya yi da Jamusanci a 1823. Fassarar Ingilishi ta fito ne tsakanin 1882-1884, wadda John Pyhne ya gabatar a Ingila, daga wannan sai fassarar Richard Burton, tsakanin 1884-1888, wadda ta kasance bakandamiya a fagen fassara a Turai, domin ta kunshi yawancin labaran da sauran masu fassara ba su yi amfani da su ba. Haka ya gyara kura-kuran da wadanda suka yi fassara kafin tasa suka tafka.

Abin lura shi ne, dukkan aikin fassarar Alfu Laila a Turai ya gudana ne tsakanin 1704 zuwa 1888, saboda haka littafin Alfu Laila na Ingilishi da ya shigo kasar Hausa daga Turai ya yi tasiri sosai, shi ne fassarar Burton. Bincike ya tabbatar da samuwar littafin a sassan kasar Hausa tun farkon karni na 20. Idan kuma aka dubi zamanin da ke tsakanin 1704 zuwa 1888, za a ga cewa tuni Musulunci ya kafu a kasar Hausa. A cikin wannan zamani ne manyan masana da malamai daga Yammacin Afirka da kasashen Larabawa suka dade da zaunawa a yankin kasar Hausar. A wannan lokaci ne aka gudanar da jihadin Shaihu danfodiyo, wanda ya kara tabbatar da ginuwar Musulunci. 

Saboda haka shigowar Musulunci, shigowar adabin Larabci da sauran al’adun Larabawa. 

Ba sai an sake nanatawa ba, littafin Alfu Laila na Larabci ya dade da zaunewa a yankin kasar Hausa, ana ma iya cewa dadewar addinin Musulunci, iya tsufansa a kasar Hausa. Wannan dadewa ita ta sa masanin nan Hiskett ya jaddada tasirin Alfu Laila na Larabci ga al’ummar Hausawa, a maimakon fassarar Ingilishi, inda yake cewa “idan aka ce za a tsaya a tattauna matsayin Alfu Laila ga al’adu da adabin al’ummomi Musulmi a duniya zai kasance bata lokaci ne kurum, domin kuwa abu ne tabbatacce, Alfu Laila ya yi tasiri ga dukkan adabin da ya ci karo da shi. Dangane da haka in ana nazarin adabin al’ummu da ke da addinin Musulunci a ruhin rayuwarsu, za a so a san daga wadanne sassa na littafin al’ummomin suka aro, har ya yi tasiri a nasu adabin. Ana jin cewa a kasar Hausa, labaran da aka gina a Misra za su fi yin tasiri fiye da wadanda aka gina a Farisa ko Indiya.” Wannan bayani ya fiddo yanayin tasirin Alfu Laila fili a kasashen Musulmi ciki kuwa har da kasar Hausa, inda daga bisani aka sami labaran littafin da yawa a tatsuniyoyin Hausa, suka zama tamkar ‘yan gida.

Mafassara Alfu Laila zuwa harshen Hausa, sun kasu kashi biyu, akwai Baturen nan Frank Edgar, (wanda ya wallafa littafi na 1 da 2 ) a 1924 da kuma wani malam Mamman Kano da ya fassara littafi na 3 da 4 da 5, duk daga Larabci suka yo fassarar ba daga Ingilishi ba. Kenan na Larabcin shi ne asasi! Idan muka alakanta wannan batu da aikin adabin kasar Hausa za mu fahimci cewa al’ummar Hausawa sun tashi da Alfu Laila, a cikin rayuwarsu, musamman a gidajen malamai da wuraren karantarwa inda aka tanadi littafin don koyar da luggar Larabci da karatun adabin da ke cikinsa.

A daidai lokacin da Frank Edgar a can Lardin Sokoto ke tattara labarai da tatsuniyoyi da tarihe-tarihen kasar Hausa ya ci karo da labaran da aka fada masa da baki, amma sai da ya bincika sai ya gane cewa ai labarai ne daga littattafan Larabawa, musamman Alfu Laila. Wannan ne ya sa ya shiga lalube, har ya gano cewa tuni an fassara littafin cikin Hausa baki dayansa.

Za Mu Ci Gaba…