✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dare Dubu Da daya (1)

Idan aka ce ba a samu aikin adabi na labari ko hikaya da ya kai na Alfu Laila tashe da karbuwa a tsakanin al’ummomin duniya,…

Idan aka ce ba a samu aikin adabi na labari ko hikaya da ya kai na Alfu Laila tashe da karbuwa a tsakanin al’ummomin duniya, da alama ba a shara ta ba. Aiki ne da ya yi tashe cikin harsuna bila adadin a cikin doron kasa. Ya nishadantar da ilimantar da fadakar da kuma koyar da fannonin adabi da suka shafi zube da waka da kuma uwa-uba, lugga da nahawu, musamman a cikin Larabci. Saboda irin tashe da karbuwa da kuma tasiri da wannan aikin adabi ya yi a doron kasa, ya sa ya zama abin sha’awa da kauna, har ya kasance idan ba a ga fassarar sa a cikin harshe ba, ake wa wannan harshe kallon uku, kwabo…. To amma asali da ginuwar wannan katafaren aiki, har yanzu cikin duhu ake.

Daga bincike-binciken da aka yi game da Alfu Laila ya zuwa yau babu wata takamaimiyar matsaya da aka samu dangane da ko wa ya rubuta wannan katafaren aikin adabi, haka kuma ba wanda zai iya tabbatar da a wane wuri ne aka tsara ko aka wallafa littafin. Shi kuwa zamani da lokaci da kuma shekarar da aka yi wannan aiki ba tabbatattu ne ba. Ta’allake da wannan kuma ba a tabbatar da su wane ne suka yi aikin tacewa da kare-karen da littafin ya samu ba cikin tsawon lokaci ba.

Ta yaya za a samu karin haske dangane da asali da ginuwar wannan katafaren aiki. Abin da ya fi dacewa shi ne a koma cikin littafin kan sa domin ganin yaya batun yake. A karshen littafin kacokam ga abin da aka ce a matsayin rufewa.

“Mun gode wa Allah da ya gwada baiwarsa ga bayinsa da barorinsa. Wannan shi ne karshen hikayar Sarki Shaharuman da matarsa Shaharuzad. Tsira da aminci su tabbata ga shugaban Annabawa da Alayensa kubutattu da sahabbansa zababbu. Wannan littafi ya cika, shi ne wanda ya tattara kyawawan labarai da abubuwan al’ajabin al’ajabai, matattarar duka dangin fannoni na labaru da hikayoyi da hadisai da wa’azi da ladabi da hankali da ilmi daga zamanoni cikin tafarkin Musulunci, abin bi da gaskiya ga mazowansa da al’adunsu, mazowan alheri. Littafi ne wanda ya kunshi abubuwan nema, mai karantawa zai samu cikar farin ciki, haka nan mai sauraren su da kunnen basira.” 

bayan nan an karkare da cewa, “Wannan littafi an rubuta shi a makarantar ilmi wadda aka sani a unguwar Dalil. Daga cikin labarun, akwai lu’ulu’un ilmi, matattarar hikayoyin masana. babban marubucinsu shi ne, Sidi Muhammadu bawan Abdulwahid, farin ciki ya tabbata gare su, shi da dan uwansa badaru Misik. An ambace su cikin karshen Rabi’us Sani, shekarar mafificin talikai tana da 326. Haskakkakiyar gaisuwa ta tabbata a gare shi. Amin!”

Daga nan tambayar da masana kan yi ita ce shin wane ne Sidi Muhammadu bawan Abdulwahid ko dan uwansa badaru Misik, wadanda suka rayu hijira na da 326. Idan har an san da su, to ke nan za a iya cewa an san ko wane ne marubucin da kuma lokacin da aka shirya aikin. To amma komawa cikin littafin da bin diddigin tarihin ginuwar sa sai a fahimci kila dai wannan lokaci da kuma marubucin da aka ambata su ne na karshe daga cikin masu tacewar wannan aiki tun asali, ba wai na farko ko kuma asalin marubutan ba.

ba wani abu ya jawo ka-ce-na-ce kan asali da wanzuwar wannan littafi ba sai cewa littafin yana kunshe ne da tatsuniyoyi da labaran ban dariya da na soyyayya da bayanai kan rayuwar gaskiya ko tarihi da tarihihi da tsunduma a cikin duniyar aljanu da maridai da ifiritai da sauran su, ba kuma a nahiyar Larabawa kadai ba, ya watayo nahiyar Asiya da kuma wasu sassa ba nahiyar Afirka.

Rashin tantance hakikanin gaskiya game da asali da marubutan littafin Alfu Laila, bai zama abin mamaki ba, domin in an duba da kyau za a ga cewa litttafi ne wanda tun farkon tsara shi har ya zuwa lokacin da ya bunkasa, ya yi bulaguro zuwa kasashe da dama, kuma ya ratso zamunna daban-daban. Ya fada hannun masu tacewa da masu sake masa kama, bila adadin. Wannan matsayi nasa ne ya sa Turawa masu nazari tun da dadewa suka kasance cikin rudu dangane da wannan littafi, wasu na cewa, “abin mamaki ne a ce aikin talifi kamar wannan da aka san shi a Turai da dadewa, aka kuma yi sama da shekara 200 ana nazarinsa, amma ba a san masomarsa ba. Sa’annan kuma ba a san sirrin da aka yi amfani da shi wajen tsara shi ba.”

Wannan ne ya sa daga binciken da aka gudanar, aka sami rukuni biyu na masana kuma mabambanta dangane da asalin wannan littafi.

Akwai masu cewa daga kasar Farisa ya fito da kuma masu cewa tsittsigensa na kasar Larabawa ne. Masu ra’ayin cewa daga kasar Larabawa ya fito sun fi kafa hujja ta nuna cewa ba wani littafin Alfu Laila a wani harshe da ya fi na Larabci dadewa a halin yanzu, haka kuma yawancin labaran da ake da su a cikin littafin a kasashen Larabawa aka tsara su, ko kuma suna dauke da sunayen Musulunci ko masu tasiri da addinin Musulunci. Haka ma wasu labaran da aka gina na cikin littafin za a ga cewa ko da an yi dace da wasu wadanda ba na Musulunci ba, ko kuma ma an tsara labarin kafin zuwan Musulunci, za a sami birbishin Musulunci a cikin su. Misali, labarin kamarzaman da Gimbiya badura, a cikin Alfu Laila a kasar Sin aka nuna an tada labarin, amma mahaifin badura Musulmi ne, mahaifiyar Sarki kamarzaman, sunanta Fatima, jama’ar kasar ma Musulmai ne, da makamantan wadannan da dama.

Su kuma wadanda suka danganta Alfu Laila da kasar Farisa sun yi haka ne ganin matsayin yankin a fagen raya adabin dauri, musamman yadda ake sane da cewa daga Farisa da Indiya ne aka bubbugo da rubuce-rubuce irin na Alfu Laila. Wannan ne ya sa ake jin cewa ainihin littafin da Farisanci aka yi shi, Larabawa kuma suka dauka suka fassara shi, domin kuwa akwai wani dadadden littafi mai kama da Alfu Laila na Larabci da harshen Farisanci da ya yi kama da Alfu Layla, wanda kuma ya girme shi da dadewa, wannan littafi shi ne Hazar Afsanah, ko kuma Labarai Dubu, wanda jama’a daga baya suka sani da Alfu Laila.

Za Mu Ci Gaba…