A lokacin da Ibrahim ya koma gida bayan kwana 7 da yi masa aure. Da shiga gidan sai ya wuce dakin mahaifiyarsa Hajiya Delu yana murna. Bayan sun gaisa sai ya fada mata abubuwan da suka faru a lokacin da yake hidimar kasa kuma ya shaida mata ya kammala lafiya yanzu abin da ya rage masa shi ne ya nemi aiki, daga nan ne zai tunkari maganar aure.
Sai dai ya lura an yi wa dakinsa kwaskwarima, don tun daga nesa ya hango dakin ya sha gyara da fenti, dakin sai sheki yake yi. Sai ya tambayi mahaifiyarsa ko mahaifinsa Malam Usman ya kara aure ne? Sai mahaifiyarsa ta amsa masa da cewa a’a, kai dai tafi ka shiga dakinka daga baya za ka ji labarin komai.
A nan ne Ibrahim ya sha jinin jikinsa, amma da yake mutum ne mai yi wa iyayensa biyayya, bai musanta ba sai ya nufi dakinsa. A lokacin da Ibrahim ke hira da mahaifiyarsa, mahaifinsa Malam Usman ba ya nan.
Yana isa dakin sai ya yi sallama, sai kuma ya ji muryar mace daga ciki ta amsa. Abin sai ya daure masa kai, duk da haka sai sai ya shiga cikin dakin. Shigarsa ke da wuya sai ya hada ido da Halima, da ma ya san ’yar uwarsa ce amma dai babu wani abu da ya taba shiga tsakaninsu a bangaren soyayya. Hasali ma yana ganin ba tsararsa ba ce musamman da yake shi ya yi karatu mai zurfi ita kuwa iyakar karatunta firamare ta yi.
Da ya tambaye ta me take yi a dakinsa? Sai ta amsa masa da cewa ai ita ce amaryarsa kuma yau kwana bakwai ke nan da aka daura musu aure. Idan kuma yana neman karin bayani ne to ya koma wajen mahaifiyarsa ya tambaye ta.
Nan take idonsa suka canja, hankalinsa ya tashi, bai san lokacin da hawaye suka rika zuba daga idonsa saboda haushi da takaici. Ya nufi dakin mahaifiyarsa yana surutai, yana furta wasu kalmomi da bai ma san abin da yake fadi ba, saboda rudewa da takaici.
Shigarsa ke da wuya ashe mahaifinsa Malam Usman ya koma gida kuma ya yi haka ne don ya kwantar wa Ibrahim rai a kan abin da ya faru. Kuma mahaifin ya hangi Ibrahim a lokacin da mai babur na haya ya sauke shi a kofar gida lokacin da ya dawo, amma shi Ibrahim bai lura da mahaifinsa ba a lokacin da suke hira a wata rumfa ba.
Da Ibrahim ya shiga dakin sai suka hada ido da mahaifinsa Malam Usman, nan take ya sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idonsa wanda hakan ya nuna bai amince da abin da suka yi masa ba, amma kuma ba zai iya jayayya da su ba.
Nan Malam Usman ya rarrashe shi, kuma ya umarci ya koma dakin amaryarsa, ya dauki abin da ya faru a matsayin kaddara ce daga Allah. Kuma idan Ya yi hakuri zai ga sakayya a wajen Allah.
Nan dai Ibrahim ya koma dakin amaryarsa Halima jikinsa ya yi sanyi. Da ya shiga dakin sai ya rasa ta inda zai fara. Da farko dai babu wata soyayya da ya taba yi da Halima. Sannan Halima a wajensa tamkar kanwarsa ce da ya sha ba ta shawara game da yadda ya kamata ta tafiyar da rayuwarta musamman a bangaren yin karatu.
Daga nan ne Halima ta rarrashe shi ta fada masa duk yadda abubuwan suka kasance daga farko har karshe. Ita ma ta nuna mahaifanta ne suka tilasta ta yin wannan aure, amma saboda ladabi da biyayya hakan ya sa ta amince.
Za mu ci gaba
Za a iya samun Ahmed a 08097015805