Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Darasi ga mahaifi’ labarin yana nuni a kan yadda da zai iya dora mahaifi a kan hanya madaidaiciya. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Malam Bello, makeri ne da ya kasance mai yawan yin shaye-shaye da rashin girmama mahaifinsa Shehu. Shehu ya tsufa sosai kuma bai da karfi saboda dansa Bello ba ya ciyar da shi yadda ya kamata.
Bello yana da da mai suna Nuhu wanda ya shaku da Kakansa Shehu kuma ba ya jin dadin yadda mahaifinsa ke wulakanta masa Kaka kuma abin yana sanya shi cikin takaici domin ba ya iya cewa komai.
Ran nan Shehu na cin abinci sai kwanon abincin ya sullube a hannunsa ya fadi ya fashe. Ganin haka, sai dansa Bello ya shiga yi masa fada kamar zai dake shi.
Washegari Nuhu ya samu katako ya sassaka kwanon cin abinci. Ko da mahaifinsa Malam Bello ya tambaye shi abin da zai yi da shi, sai ya ce ya sassaka kwanon cin abincin ne saboda idan Malam Bello ya tsufa ya rika zuba masa abinci a ciki, don gudun kada idan kwanon ya subuce a hannunsa ya yi masa fada kamar yadda ya ga yana yi wa Kakansa Malam Shehu.
Wannan kalami da Nuhu ya yi, ya girgiza mahaifinsa Malam Bello inda nan take ya gane kurensa ya yi niyyar ba zai sake wulakanta mahaifinsa Malam Shehu ba.
Da fatan Manyan Gobe sun dauki darasi daga wannan labari.