✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darajar Naira ta sake samun koma baya

Naira ta zama ta ɗaya a cikin ƙasashe mafi lalacewar darajar kuɗaɗe a watan da ya gabata.

Darajar kuɗin Nijeriya na Naira ya ci gaba da faɗuwa a ƙarshen wannan mako inda farashin duk Dalar Amurka ɗaya ya koma N1,510 a kasuwar ’yan canji yayin da a hukumance farashin ya tuƙe kan N1,466.31.

Farashin canjin dalar zuwa naira ya ƙaru da N40 a tsakanin ranar Alhamis da Juma’a, bayan da aka rufe kasuwa a farashin Dalar kan N1,426 a cewar Hukumar Canjin Kuɗaɗen Ƙetare ta NAFEM.

Wannan faɗuwar darajar Nairar na zuwa ne duk da tsauraran matakan da Babban Bankin Nijeriya CBN ya shimfiɗa a bayan nan domin ganin darajar kuɗin ya haɓaka har ta kai ga ana canjin duk Dala ɗaya kan ƙasa N1,000.

Babban Bankin ya kuma riƙa bai wa ’yan canjin kuɗaɗen ƙetare domin bunkasa harkokin kasuwa da tattalin arzikin ƙasar.

Sai a safiyar Juma’ar da ta gabata, an riƙa sayar da Dala ɗaya kan N1,450 amma ya zuwa Yammaci gabanin rufe kasuwa farashinta ya koma N1,510.

Wani ɗan canji da ya zanta da Aminiya a ranar Asabar, ya ce buƙatar Dalar Amurka ta ƙaru matuƙa a ’yan kwanakin nan, lamarin da ya sanya farashinta ya tashi.

“Ina mai tabbatar muku da cewa a yanzu haka Dalar ta yi ƙaranci kuma wannan ya sanya farashinta ya ƙara tashi.

Tun dai a watan Janairun bana ne Kafar watsa labarai da fashin baƙi kan harkokin kasuwanci ta Bloomberg ta yi hasashen cewar darajar Naira ta Najeriya za ta samu koma baya a 2024 wanda ba a taɓa gani ba tun bayan da Nijeriyar ta dawo mulkin dimokuraɗiyya a 1999.

A cikin rahoton da ta fitar Bloomberg ta ce duk da yawan faɗuwa da darajar Naira ta yi a 2023, Nairar za ta sake fuskantar koma bayan daraja a 2024, irin koma bayan da ba a taɓa samu ba tun da kasar ta koma mulkin dimukuradiyya a 1999.

Wannan koma baya da Nairar ta Nijeriya ke fuskanta, ya sa ta zama ta ɗaya a cikin ƙasashe mafi lalacewar darajar kuɗaɗe a watan da ya gabata.