✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darajar Naira ta farfado zuwa 900 a kan kowacce Dala

Wannan ne karon farko da Dalar ta sauko kasa da N1,000 a cikin wata guda

Darajar Dalar Amurka ta fadi warwas a ranar Juma’a, inda Naira ta fafado zuwa kasa da 1,000 a kasuwannin bayan fage.

Wannan ne dai karo na farko a cikin sama da wata guda da Naira ta farfaɗo, bayan a baya ta haura sama da N1,000 a kan kowacce Dala.

Daga N1,150 da aka sayar da Dala a kasuwannin a ranar Alhamis, ya zuwa ranar Juma’a an sayar da ita har 950, inda ta fadi da sama da N200.

Majiyoyi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas sun tabbatar wa wakilinmu cewa an canzar da kowacce Dala daga tsakanin N750 zuwa N800 da safe, kafin ta kai N950 zuwa yamma.

Hakan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta bakin Babban Bankin Najeriya (CBN) suke cewa sun fara tunkuda wasu kudade har kimanin Dalar Amurka biliyan bakwai domin farfaɗo da darajar Nairar.

Wani dan canji a Legas mai suna Abu Dollar, ya ce, “Yanzu haka maganar da muke yi da kai, N950 muke sayar da Dala. Ban san me zai faru ba nan da safiya. Jiya N1,150 ce, yau kuma ta karye zuwa N950 a nan.

“Idan Allah Ya kai mu gobe, kawai ka kira ni zan fada maka halin da kasuwar ke ciki,” in ji Abu.

Shi ma wani mai sana’ar canjin a filin jirgin na Legas mai suna Malam Ubaida, ya ce, “Yau da yammacin nan, mun sai Dala a kan N900. Amma da safe har N800 mun saye ta. Hakan na ta faru ne saboda abin da CBN yana yi,” in ji shi.

Sai dai ya shawarci babban bankin da ya samar da isasshiyar Dalar ga kai tsaye ga ’yan canji, inda ya ce yin haka zai sa darajar Naira ta sake farfadowa.