✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Darajar Naira: Dalar Amurka ta kai N421 a kasuwar bayan fage

Wannan dai shi ne farashi mafi tsada a kwanakin nan

Darajar Naira ta kara faduwa kasa a kasuwar bayan fage, inda aka yi musayar kowacce Dalar Amurka kan Naira 421 a ranar Laraba.

Hakan na nuni da cewa Nairar ta sake faduwa sabanin a ranar Talata da aka yi canjinta Dala kan Naira 420.

Budadden farashinta dai ya tashi ne kan Naira 149 kowacce Dala a ranar Laraba.

Kazalika, farashin na Naira 444 kan Dala daya shi ne mafi tsada da aka samu ranar Larabar, kafin ya daidaita kan Naira 421.

Haka kuma an canja ta a farashi mafi karanaci na Naira 412 Dala daya, a ranar Larabar.

Jumullar Dala miliyan 72 dai aka yi ciniki a musayarta a kasuwar bayan fage ta ranar Larabar.