✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Darajar kwallayen gida da waje a gasar Zakarun Turai ta zama daya — UEFA

Darajar kwallayen gida da waje a gasar Zakarun Turai ta daidaita.

Hukumar Kwallon Kafar Turai ta UEFA, ta ce a yanzu an daidaita darajar kwallayen gida da waje a wasannin gasar Zakarun Turai.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Shugaban Hukumar Alexander Cefrin ya fitar a ranar Alhamis, da ta ce matakin zai soma aiki a sabuwar kakar wasan da za a shiga ta 2021/2022.

Ceferin ya ce da wannan mataki an kawo karshen muhawarar da aka share shekaru ana yi kan rashin adalcin da wasu ke zargin na tattare da dokar daga darajar kwallayen da kungiya ke ci a wajen gidanta.

Sanawar ta ce matakin na UEFA na nufin daga yanzu idan kungiyoyi suka yi kankan wajen cin kwallaye fafatawarsu a gida da waje, za a basu karin mintuna 15 domin sake karawa, idan kuma damar ta faskara sai a kai ga zagayen bugun daga kai sai mai tsaron raga wato Fenareti.

Alkaluma na tarihin sun ce tun daga shekarar 1965 ake amfani da dokar banbanta darajar kwallayen gida da waje a gasar cin Kofin Zakarun Turai, lokacin da ake kiran gasar da European Cup, kafin daga bisani a sauya sunanta zuwa Champions Leagu a kakar wasa ta 1992/1993.