Rahotanni daga Rasha sun bayyana cewa darajar takardar kudin kasar na Ruble ta karu a kasuwannin hannayen jari a makon nan.
Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce ba zai sake karbar kudin Yuro ko Dala, na cinikin da Turai take yi wajen sayo iskar gas daga Rashar ba.
- Birtaniya ta amince Chelsea ta sayar da tikitin kallon wasanni
- Al-Shabaab ta kai tagwayen hare-hare a Somalia
Putin ya ce, ya bai wa kasashen na Turai wa’adin mako guda, su samar da wani tsarin da za su biyan kudin gas din da kudin Ruble na Rasha a maimakon kudin Yuro ko Dala da suke biya da shi.
Shugaban na Rasha ya bukaci babban bankin Turai da gwamnati da su kafa wani sabon tsari wanda dole ya kunshi sayan Ruble a kasuwannin musayar kudi.
Wannan sanarwar dai ta yi tasiri nan da nan a kan kudin kasar na Rasha, wanda ya tashi a kasuwannin hannayen jari fiye da kudin Yuro da Dala.
Fadar shugaban kasar Ukraine ta yi Allah wadai da yakin tattalin arziki da Moscow take yi don karfafa kudinta na Ruble.