✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dani Alves ya sake komawa Barcelona

A shekarar 2008 ce Alves ya koma Barcelona karon farko daga Sevilla.

Dani Alves, dan wasan baya na kasar Brazil, ya sake komawa Barcelona bayan shekaru biyar da rabuwa da kungiyar.

A yammacin Juma’ar da ta gabata ce kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cimma yarjejeniyar sake daukan dan wasan mai shekara 38 a kyauta.

Wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta, ta siffanta Alves a matsayin dan wasan baya na gefen dama mafi kwarewa a tarihinta.

Sanarwar ta ce Alves zai fara daukar hora a Barcelona a mako mai zuwa amma ba zai iya buga wasa ba har sai watan Janairu.

Dani Alves

A bayan nan ne kungiyar ta bayyana ra’ayin kin daukar dan wasan, amma sabon kocinta, Xavi Hernandez ya nuna sha’awar dawo da shi tawagar domin taimaka mata dawowa kan ganiya.

A watan Satumba aka dakatar da kwantiraginsa a kungiyar Sao Paulo sakamakon tababar da ta dabaibaye batun albashinsa.

Alkalumma na tarihi na cewa, Alves ya fi kowane dan wasan lashe gasa da kofuna iri-iri ciki har da manyan gasa 9 da ya lashe a Barcelona, Juvenstus da Paris St-Germain.

Alves wanda ya shafe shekara takwas a Barcelona daga shekarar 2008 zuwa 2016, ya lashe La Liga shida da Zakarun Turai uku da kuma Copa del Rey hudu da sauran kofuna da a jimulce sun kai kusan 23.

A shekarar 2008 ce Alves ya koma Barcelona karon farko daga Sevilla.