✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dangote zai gina kamfanin suga a Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta ce rukunin kamfanonin dangote ya kuduri aniyyar gina kamfanin sarrafa suga a jihar, wanda zai ci kimanin Naira biliyan 148.Gwamnan Jihar,…

 Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani BelloGwamnatin Jihar Neja ta ce rukunin kamfanonin dangote ya kuduri aniyyar gina kamfanin sarrafa suga a jihar, wanda zai ci kimanin Naira biliyan 148.
Gwamnan Jihar, Alhaji Sani Bello shi ne ya yi furucin ta bakin mataimakinsa, Ahmad Muhmmad Ketso a taron da gwamnatin ta yi da jami’an rukunin kamfanonin dangote da al’ummar kauyukan Jima-Nupeko da ke karamar Hukumar Mokwa, inda kamfanin zai gina masa’antar sugan.
Taron wanda aka yi shi a fadar Etsu Nupe da ke garin Bida ya zo ne daidai lokacin da kamfanin dangote ya nuna sha’awarsa na mallakar katafaren fili mai girman hekta dubu 16, inda zai yi noman rake da kuma sarrafa suga a jihar.
Gwamnan ya bayyana hanyar da gwamnatin jihar za ta samar da ayyukan yi ga daukacin matasa a jihar shi ne ta hanyar karfafa gwiwar masu zuba jari.
Hakan ya ce zai taimaka kwarai wajen bunkasa tattalin arzikin jihar da rage rashin aiki tare da rage barna a jihar.
Gwamnan ya roki masu zuba jari musamman wadanda suke bangaren noma su zo su ci moriyar arzikin jihar ta hanyar zuba jarinsu a jihar.
Taron ya kafa kwamitin da zai yi nazarin abubuwan da za su taimaka wajen samun nasarar kafa kamfanin, sannan kuma ya bayar da rahotonsa cikin makonni shida.
A bangare daya kuma an umarci ofishin Lauyan Gwamnatin Jihar ya tsara takardar yarjejniya kafin taro na gaba.
Shugaban tsare-tsare na kamfanin sarrafa suga na dangote, Murtala Zubairu ya yaba wa matakan da gwamnatin jihar ta dauka don ganin kamfanin ya samu nasarar burin da ya sanya a gaba.
Ya bayyana cewa aikin kafa kamfanin zai gudana mataki-mataki, kuma ya ce za su fara shuka rake ba tare da bata lokaci ba.
Zubairu ya bayar da tabbacin cewa kamfanin dangote kamfani ne da ke sauke nauyin da yake kansa, sannan kuma ya yi alwashin cewa kamfanin ba zai yi watsi da mutanen kauyen da ke makwabtaka da shi ba a jihar.