✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote ya bukaci a fitar da Arewa daga kangin talauci

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bukaci gwamnoni da shugabanin Arewa su yi kokarin wajen fitar da yankin daga kangin talauci, bayan ya…

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bukaci gwamnoni da shugabanin Arewa su yi kokarin wajen fitar da yankin daga kangin talauci, bayan ya bayyana  yankin da cewa shi ne kan gaba wajen talauci.

Alhaji Aliko Dangote ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen wani taron bita kan zuba jari da gwamnatin jihar Kaduna ta shirya a karshen makon jiya, inda ya ce, akwai bukatar gwamnatocin jihohin Arewa su tashi tsaye wajen ganin sun cike gibin kasuwanci da ci gaba da ke tsakaninsu da Kudancin kasar nan.

Ya dora wa gwamnonin Arewa laifi kan kin tabuka wani abin a zo a gani don kawar da talauci a Arewa.

“Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas kashi 60 na mazauna yankin na cikin matsanancin talauci. Akwai bukatar a sani cewa jihohi 19 da ke Arewa wadanda kuma suke da kashi 54 na yawan jama’ar kasar nan kuma suke da kashi 70 na fadin kasa, kashi 21 kacal suka iya samarwa na kudaden shiga a kasar nan a shekarar 2017.

Yankin Arewa zai ci gaba da kasancewa a baya muddin gwamnonin yankin ba su yunkura wajen cike wannan gibi na ci gaba da ke tsakaninsu ba. Wannan ya sa muke cewa babban kalubalen da muke da shi, shi ne mu samu akalla gwamnoni goma irin Malam Nasir El-Rufa’i da za su taimaka wajen ciyar da Arewacin Najeriya gaba,” inji shi.

Alhaji Aliko Dangote ya ce cike wannan gibi na bukatar zuba jari na shekaru kuma gwamnati kadai ba za ta iya samar da wadannan kudade ba. Kamfanonin masu zaman kansu ne kawai za su iya samar da irin wadannan kudade na zuba jari domin samar da ci gaba da kasar nan ke bukata.

Ya bayyana cewa dole ne a samar da yanayi mai kyau da zai jawo masu zuba jari domin su shigo su zuba jarinsu don kawo ci gaba a yankin.

“Kamfanoni masu zaman kansu za su samar da ayyukan yi domin kawar da manyan matsalolin yankin wato talauci da rashin aikin yi. Idan mutane masu yawa suka samu aikin yi, za a samu raguwar aikata miyagun ayyuka a cikin al’umma musamman a tsakanin matasa,” inji shi.

Ya shawarci sauran jihohin Arewa su yi koyi da Gwamnan Jihar Kaduna wajen inganta hanyoyin zuba jari domin bunkasa tattalin arzikin yankin.

Yadda za ka zama kamar ni- Dangote

A wani bangaren kuma, Dangote wanda shi ne ya fi kowa dukiya a Nahiyar Afirka ya bai wa matasan nahiyar shawarwari idan suna son zama kamarsa.

Hamshakin attajirin ya bayyana haka ne lokacin wata hirar musamman da ya yi da attajirin nan dan kasar Sudan Mo Ibrahim a birnin Abidjan na kasar Kwaddibuwa karshen makon jiya.

Wani mahalarcin taron ya tambayi attajirin wadanne bangarori zai fi mayar da hankali idan aka ce yana a matsayin dan shekara 21 da haihuwa kuma yana shirin fara kasuwanci.

Dangote ya ce zai fi mayar da hankali ne a harkarkokin sadarwa na zamani da kuma aikin gona.  “Wadannan ne bangarori biyu da za su fi kawo riba,” inji shi kamar yadda BBC ya ruwaito.

Daga nan ya ja kunnen matasa game da dabi’unsu bayan fara kasuwanci musamman ’yan Afirka. Ya ce muna “Kashe ribar da ba ta kai ga zuwa hannunmu ba. Da zarar ka fara kasuwanci kuma kasuwancin ya fara samun ci gaba, maimakon ka yi ta kara uwar kudin, sai mutum ya fara kashe kudin da tunanin ribar za ta ci gaba da zuwa,” kamar yadda ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa, “Dole ne mutum ya natsu saboda akwai kalubale nan da can.”

Attajirin ya ce bai kamata mutum ya fara kashe kudi ba ba-ji-ba-gani ba.

“Saboda idan ka sayi manyan abubuwan more rayuwa (kamar motocin kawa) za su dauke maka hankali daga harkokin kasuwancinka,” inji shi.

Daga nan, ya bayar da misali da kansa, inda ya ce “Ba ni da wani gidan shakatawa mallakina a ko’ina a fadin duniya.”

“Amma akwai wadansu daga cikin ma’aikatana da suke da gidan shakatawa a birnin Landan,” inji shi.

Na taba ciro Dala miliyan 10 lakadan daga banki – Dangote

Alhaji Aliko Dangote ya ce ya taba zuwa banki inda ya karbo Dala miliyan 10 (kimanin Naira miliyan 360) domin ya tabbatar da cewa da gaske yana da kudin.

Dangote ya ce da ya je bankin, ya rubuta takardar karbar kudi sai ya karbi kudin lakadan sa’annan ya zuba su a bayan motarsa. Sai dai ba kashe kudin ya yi ba, “Washegari na mayar da su banki domin ci gaba da ajiyarsu,”inji shi.

Da aka tambaye shi nawa yake da shi a cikin aljihunsa a lokacin hirar, sai ya ce “Za ka yi mamaki. Babu ko sisi a aljihuna, ko Dala daya babu a ciki.”

‘Najeriya za ta zama kasa ta biyu da ta fi fitar da man fetur’

Dangote ya ce aikin gina matatar man da yake yi a Legas zai ci kimanin Dala biliyan 12 zuwa 13.  Ya ce idan aka kammala gininta za ta rika samar da gangan mai dubu 650, a kowace rana.

Ya ce idan aka kammala ta, hakan zai mayar da Najeriya kasa ta biyu da ta fi fitar da man fetur a Kudu da saharar Afirka.

“Babban kalubalen da muka fuskanta lokacin fara gina matatar shi ne sai da muka gina tashar jirgin ruwa ta musamman saboda babu wata tashar jirgin ruwa a kasar nan da za mu iya shigo da manyan na’urorinmu ta ita.”

A bangaren siminti, Dangote ya ce a bana Najeriya za ta kasance kasar da ta fi kowace fitar da shi a Nahiyar Afirka.