Emmanuel Tagoe, shahararren dan damben Boksin ne a kasar Ghana, kuma ya ce dan da matarsa ta haifa masa mai kimanin shekara 14 ba nasa ba ne.
dan damben ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta wuce a lokacin da yake hira da manema labarai a kasar Ghana.
Ya ce tun lokacin da matarsa ta haifa masa yaron, hankalinsa bai kwanta ba, don tun farko tana da matsalar haihuwa kuma bai san yadda aka yi har ta samu ciki ba. Ya ce bayan sun rabu da matarsa ta koma gidan iyayemta ba a dade ba sai ’yan uwanta suka sanar da shi cewa ta haifi da namiji.
Hakan ya ba shi mamaki, don ya tabbatar a lokacin da suka rabu da ita ba ta dauke da juna biyu.
Sai dai bayan da ta haihu ya yi kokarin daukar dan zuwa asibiti don a yi musu gwajin kwayar hallittar jini (DNA) amma sai mahaifiyar Tagoe ta hana shi. Ta ce idan ya kuskura ya yi haka zai iya kawo rigima a tsakaninsa da tsohuwar matarsa.
Ya ce ya fara zargin matarsa ce inda hakan ya sa ya dauki matakin yin gwajin, bayan ta rika karbar makudan kudi a wajensa don kula da yaron. Ya ce a wata yakan ba ta kimanin Naira dubu 500 don kula da yaron a tsawon wadannan shekaru.
“Tunda aka haifi yaron kimanin shekara 14 da suka wuce Allah kadai Ya san irin makudan kudin da tsohuwar matata ta karba a wajena don kula da yaron. Uwar yaron ta tilasta mini sanya shi a wata makaranta mafi tsada inda ’ya’yan masu kudi irin su dan kwallon Ghana Asamoah Gyang suke kai ’ya’yansu duk da ta san ban kai su hali ba.”
Tagoe ya ci gaba da cewa da ya ga abin ya ishe shi ne, sai ya dauki yaron zuwa wani asibiti ba tare da sanin kowa ba inda aka yi musu gwajin jini da na halitta (DNA) kuma sakamako ya tabbatar yaron ba dansa na cikinsa ba ne.
Da aka tambaye shi matakin da zai dauka a yanzu sai ya ce, ya bar wa Allah. Kuma ya ce shi bai ga laifin yaron ba, kuma duk kudin da ya kashe a kan yaron har zuwa yanzu, ba zai nemi a biya shi ba. “Abin farin ciki shi ne yanzu na fita daga kangin daukar nauyin dan da ba nawa ba,” inji shi.