✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan Yahoo ya kashe makwabciyarsa a gidan haya

Wani matashi da ake zargi mai damfara ta intanet (Yahoo) ne ya kashe makwabciyarsu ya sanya gawarta a cikin jakar Ghana-Must-Go

Wani matashi da ake zargi mai damfara ta intanet (Yahoo) ne ya kashe makwabciyarsu a gidan haya.

Matashin mai shekaru 25 ya sanya gawarta a cikin jakar Ghana-Must-Go, ya kai wani kango ya boye.

Wanna lamari dai ya auku ne a yankin Ore da ke Karamar Hukumar Odigbo a Jihar Ondo.

Wani ganau ya ce an kama matashin ne bayan an yi cigiyar matar a unguwar.

Ya ce “Mun girgiza da jin cewa dan Yahoo din ya kashe matar domin tsafi.”

Abin ya fusata matasan unguwar suka kona gidan iyayensa.

Kakakin ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce rundunar tana tsare da wanda ake zargin.

Funmilayo ce ana ci gaba da binciken sa a hedikwatar rundunar da ke garin Akure.
Ta ce an gano gawar ce a wani kango kusa da gidan da hayan, bayan iyalan matar sun shiga neman ta.
“An fara zargin matashin ne bayan ’yar uwar matar ta ga jini a kafarsa a lokacin da suke neman ta,” in ji Funmilayo.