✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan wasan Najeriya Taiye Taiwo ya cika shekara 34 a duniya

A yau ne tsohon dan wasan Najeriya Taiye Taiwo ya cika shekara 34 a duniya. Dan wasan yana cikin ’yan wasan Najeriya da suka dade…

A yau ne tsohon dan wasan Najeriya Taiye Taiwo ya cika shekara 34 a duniya. Dan wasan yana cikin ’yan wasan Najeriya da suka dade suna taka leda a kasar waje. Ya buga kwallo a kusan kungiyoyi akalla guda 9 a yankin Turai.

Kungiyoyin da ya buga sun hada da: Marseille, da AC Milan da QPR, da Dynamo Kiev da Bursaspor da HJK Helsinki da Lausanne da AFC Eskilstuna da RoPS.