✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan wasan Manchester United Pogba ya kamu da coronavirus

Fitaccen dan wasan tsakiya kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya kamu da cutar COVID-19 kamar yadda mai horas da ’yan wasan kwallon kafa na Faransa,…

Fitaccen dan wasan tsakiya kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya kamu da cutar COVID-19 kamar yadda mai horas da yan wasan kwallon kafa na Faransa, Didier Deschamps ya sanar.

Dalilin da haka ya sanya aka zare shi daga jerin tawagar ’yan wasan kasar Faransa da za su fafata a gasar Nations League bayan sakamakon gwaji ya tabbatar yana dauke da kwayoyin cutar.

An maye gurbin dan wasan da Eduardo Camavinga, dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Rennes.

Rahoton da jaridar L’Equipe ta wallafa ya nuna cewa Faransa za ta tunkari ’yan tawagar kasar Sweden a gasar Nations League da za su fafata a watan Satumba ba tare da tauraron dan wasan ba.

%d bloggers like this: