Kungiyar kwallon kafa ta FRSC Abuja ta Hukumar Kiyaye Hadurra ce, ta yi rashin dan wasanta na gaba mai suna Nura Suleiman.
Marigayi Nura ya rasu ne ranar Talata a lokacin da yake tsaka da wasan motsa jiki a mahaifarsa da ke garin Suleja a Jihar Neja.
Da yake tabbatar da rasuwarsa, mataimakin mai horas da ’yan wasan kungiyar Emmanuel Okocha David, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Tare da alhini ina bakin cikin sanar da mutuwar daya daga cikin ’yan wasanmu (FRSC FC, Abuja) NURA SULEIMAN.
“Ya fadi ya rasu a yayin da yake wasan motsa jiki ranar Talata da maraice a garin Suleja inda can ne mahaifarsa. Muna rokon Allah Ya gafarta masa.”
Shi ma da yake tsokaci game da rasuwarsa, daya daga cikin abokan wasansa a kungiyar ta FRSC, Nieketien Shadow Godfrey ya ce, “Mun kadu da jin rasuwar abokin wasanmu Nura wanda dan wasan gaba ne mai basira da hazaka. Hakika za mu yi rashin sa ganin ya bar gibi mai wuyar cikewa”, inji shi.
Nura Suleiman ya fara kwallonsa ne a kungiyar kwallon kafa ta Potters da ke Suleja kafin likafarsa ta ci gaba ya koma kungiyar kwallon kafa ta Niger Tonadoes.
Ya kuma buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasa ’yan kasa da shekara 23 da kungiyar kwallon kafa ta Kaduna United.
Majiyarmu ta tabbatar mana cewa bai fadi yana fama da wata rashin lafiya ba kafin ya fita wajen wasa.
An dai yi masa sutura a garinsa na haihuwa kamar yadda addinin Islama ya tanadar.