✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan wasan Denmark, Eriksen ya fadi sumamme ana tsaka da wasa

Lamarin dai ya sa dole aka dakatar da fafatawar tun a zagayen farko.

Dan wasan Denmark, Christian Eriksen ya fadi sumamme ana tsaka da kece raini tsakanin kasarsa da kuma Finland a birnin Copenhagen ranar Asabar.

Lamarin dai ya sa dole aka dakatar da fafatawar tun a zagayen farko.

’Yan wasan kasar ta Denmark dai sun rika fashewa da kuka lokacin da ma’aikatan lafiya ke kokarin ficewa da dan wasan wanda kuma yake taka leda a kulob din Inter Milan.

“Mun dakatar da gasar EURO ta 2020 saboda matsalar da aka fuskanta ta rashin lafiyar dan wasa,” inji Hukumar Wasannin Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) a cikin wata takaitacciyar sanarwa.

Filin wasa na Parken Stadium inda wasan yake gudana wanda kuma faruwar lamarin ke cike da shewa ya kasance shiru bayan dan wasa mai kimanin shekaru 29 a duniya ya fadi, yayin da sauran abokan wasan nasa suka yi masa kawanya.

Magoya bayan kulob din dai wadanda ke cikin filin wasan, cike da shaukin ganin kasar tasu ta kai bantenta a gasar, sun yi shiru cikin rashin tabbas yayin da suke dakon bayanai kan lafiyar dan wasan.

Sai dai daga bisani rahotanni sun ce dan wasan yana murmurewa a asibiti bayan ya yanke jiki ya fadi a lokacin da kasarsa ke karawa da kasar a yammacin ranar Asabar.

Dan wasan dai ya yi magana ne ta wayar tarho da sauran tawagar ’yan wasan kasarsa.

Hakan ya ba su kwarin gwiwa tare da samun saukin komawa filin wasan don ci gaba da wasan da aka dakatar sakamakon suman da dan wasan yayi.

Za a ci gaba da wasan tsakanin kasar Denmark da Finland da misalin karfe 8:30 na daren ranar Asabar.