Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ansu Fati, ya goge tarihin da aka kafa a kasar Spain na shekara 95 bayan ya zamo dan shekara 17 da ya yi nasarar zura kwallo a raga.
Dan wasan ya jefa kwallo a koma yayin wasansu na gasar cin Kofin Kasashen Turai (Nations League) wanda Spain ta lallasa Ukraine da ci hudu da nema a ranar Lahadi,
Ansu Fati wanda ya zura kwallon tasa a minti na 32 da fara wasa baya ga wannan tarihin ya kuma kafa tarihin zamowa dan wasan mafi karancin shekaru da ya zura kwallo a gasar cin Kofin Zakarun Turai da kuma La Liga a kakar wasa da ta gabata.
- Gasar Firimiya: Arsenal ta ci Fulham 3-0 a wasan farko
- Jadawalin Gasar Firimiyar Ingila na Makon farko
Yayin wasan na ranar Lahadi, ta sanadin Fati ne Spain ta samu bugun finareti wanda Sergio Ramos na Real Madrid ya zura kwallon tun a minti na 3 da fara wasa kafin ya kara kwallo ta biyu a minti na 29.
Nasarar zura kwallo biyu da Ramos mai tsaron baya a kungiyar Real Madrid ya nuna cewa yana da kwallo 10 a jere da ya zura wa Spain cikin wasa 15 a baya-bayan nan yayin da yake da jimillar kwallo 23 daidai da Afredo di Stefano.
Shi ma dai sabon dan wasan da kungiyar Manchester city ta saya Ferran Torres, da ya shiga fili bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ya jefawa Spain kwallonta ta 4 a minti na 84 na wasan.
Ansu Fati, haifaffen Guinea-Bissau da suka koma birnin Sevilla da mahaifansa tun yana da shekara 6, nasarar tasa ta goge tarihin Juan Errazquin, wanda ya zura wa Sifaniya kwallo a 1925 yana da shekara 18.