✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan uwan Shugaban Amurka Donald Trump ya rasu

Gwamnatin Amurka ta sanar da rasuwar kanin Shugaba Donald Trump mai suna Robert bayan fama da rashin lafiya a wani asibiti da ke birnin New…

Gwamnatin Amurka ta sanar da rasuwar kanin Shugaba Donald Trump mai suna Robert bayan fama da rashin lafiya a wani asibiti da ke birnin New York.

An kwantar da Robert Trump mai shekaru 71 a asibiti ne bayan ya samu matsala a kwakwalwarsa bayan wata faduwa da ya yi a baya-bayan nan.

“Cikin alhini ina sanar da rasuwar dan uwana shakiki”, inji Shugaba Trump a sanarwar da Fadar White House ta fitar.

Shugaba Trump ya ce Robert “ba dan uwana ba ne kawai, amini ne. Za a yi matukar kewar sa kuma ba zan taba manawa da kai ba Robert”.

A ranar Juma’a Shugaba Trump mai shekaru 74 ya je dubiyar marigayi Robert a asibitin da aka kwantar da shi.

A ‘yan kwanakin nan kafin ya fara rashin lafiya, Robert Trump ya shigar da karar neman kotu ta hana wata ‘yar uwarsa Mary ta buga wani littafi da ta rubuta a kan Shugaba Trump.

Sai dai bai yi nasara a karar da ya shigar ba.