Allah Ya yi wa yayan Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III rasuwa.
Alhaji Buhari Abubakar III ya rasu ne ranar Juma’a a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, bayan fama da rashin lafiya.
- ’Yar Sardauna, Aisha ta rasu
- KASU: Nan gaba za mu sanar da karin kudin makarnata
- Gwamnatin Zamfara ta rufe Kasuwar Dansadau
Kafin rasuwarsa, Alhaji Buhari Abubakar III shi ne Hakimin Sakkwato ta Arewa.
Rasuwar tasa ita ce babba ta biyu da aka yi a gidan sarautar Masarautar Daular Usmaniyya a rana guda.
Tun da farko Aminiya ta kawo rahoton rasuwar ’yar Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello, mai suna Aisha.
Sardauna Ahmadu Bello, jika ne ga Sarki Muhammadu Bello, wanda da ne ga Shehu Usmanu Danfodiyo, wanda ya assasa Daular ta Usmaniyya.
Hajiya A’i, kamar yadda aka fi sanin ta, ta rasu tana da shekara 76, a asibiti a birnin Dubai na Haddaddiyar Daular Larabawa, inda aka yi jinyar ta, Hassan Dambaba, ya sanar.
Marigayiyar, ita ce ta biyu a cikin ’ya’yan marigayi Sardauna, kuma mata ce ga marigayi Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmad Danbaba.