Dan uwan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan din nan da aka sace, Mista Jephthah Robert Yekorogha, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da shi bayan shafe kwana 14 a hannunsu.
Wasu masu garkuwa da ke dauke da muggan makamai ne suka sace shi ranar 24 ga watan Janairun 2022 a gidansa da ke Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.
Sun dai dauke shi ne zuwa wani waje da ba a sani ba, kuma sai da suka shafe tsawon lokaci kafin su tuntubi iyalansa.
Iyalan nasa dai da farko sun roki masu garkuwar da su sako Mista Jephthah ba tare da wani sharadi ba kuma ba tare da sun cutar da shi ba.
Dan uwan Mista Jephthah, kuma mai magana da yawun shugaban kamfanin Zeetin Engineering, Mista Azibola Robert, ne ya tabbatar da kubutar tasa ranar Litinin.
Sai dai bai bayyana ko sun biya kudin fansa kafin su karbo shi ba, ko kuma a’a.
Ya ce, “Muna godiya ga Allah saboda dawowar dan uwanmu, Jephthah Robert Yekorogha, daga hannun masu garkuwa.”
Kazalika, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda shi ma ya tabbatar da sako shi, amma ya ce har yanzu babu cikakkun bayanai a kan lamarin.