Allah Ya yi wa dan uwan Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, Shehu Bagudu rasuwa.
Shehu Bagudu ya rasu yana da shekaru 55, bayan gajeriyar jinya a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja.
Za a jana’izarsa da misalin karfe 11 na safiyar ranar Labara, a Babban Masallacin Birnin Tarayya Abuja.
Sanarwa ta fito ne daga shafin Twitter Gwamnan Jihar Kebbi a daren ranar Talata.