✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan uwan dan sanda ya kashe shi ya tsere da bindigarsa

Ya dirka wa dan sandan har a harabar bankin da dan sandan yake gadi

Dan uwan wani dan sanda ya harbe shi har lahira sannan ya yi awon gaba da bindigarsa.

Dan sandan da ke gadin wani banki ya gamu da ajalinsa a hannun dan uwan nasa ne a yayin da suke shirin cin abincin rana a harabar bankin da dan sandan yake gadi.

Majiyarmu ta ce abin ya faru da dan sandan mai mukamin kofur  ne a ranar Laraba lokacin da, “dan sandan ke wanke cokulan da za su ci abinci, bayan ya bar bindigarsa a bisa benci.

“Sai makashin nasa ya dauki bindigar ya matsa kusa da shi sosai ya dirka masa harbi.

“An kai shi Cibiyar Lafiya ta Gwamantin Tarayya, amma washegari ya rasu.”

Majiyarmu ta ce a makon jiya ne  dan sandan ya gabatar makashin nasa a matsayin dan uwansa ga jami’an bankin da ke Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.

Majiyar ta ce wanda ake zargin ya rika zama tare da dan sandan a harabar bankin kafin ya yi wannan aika-aika.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya kara da cewa an gano wanda ake zargin kuma rundunar za ta fara “gudanar da ba bincike domin cafko shi.”