A yayinda al’ummomi da dama a Najeriya ke fama da matsalar rashin asibitoci, wani dan tireda ya gina wa al’ummar unguwarsu asibiti kyauta.
Dan tiredan mai shekara 38 mai suna Kawu Muhammad ya sanya wa asibitin da ya gina wa al’ummar unguwarsu ta NEPA suna Al-Zunnur Clinic.
Unguwa ta NEPA da ke kan Titin Zariya a garin na Jos na da wuraren gyara da ajiya da kuma sayar da karafunan manyan motoci.
Unguwar ta hada mazauna daga sassan Najeriya saboda yanayin harkokinta amma duk da haka ba ta da asibiti.
- Tsohon Shugaban Asibitin Mallam Aminu Kano ya rasu
- Nan da wata biyu za a samu rigakafin COVID-19 –WHO
A hirarsa da Aminiya kan asibitin da aka bude a makon da jiya, Kawu Muhammad ya ce shi haifaffen Layin Inuwa Kano ne a garin Jos, amma zama ya kawo su NEPA.
- Abin da ya sa na gina asibitin
Ya ce abin da ya ba shi karfin gwiwar gina asibitin shi ne irin mawuyacin halin da al’ummar unguwar ke fuskanta saboda rashin asibiti.
Kawu ya ce, “Wata rana da misalin karfe biyu na dare nakuda ta kama matar makwabcina; Haka suka dauke ta a mota zuwa garin Yalwa da ke nesa da unguwar, suka kai ta asibiti cikin wahala”.
Wannan abu, a cewarsa, ya sa shi sayar da kadarorinsa ya fara aikin gina wannan asibitin.
- Na sa wa ’yan uwana haraji
Sai dai kadarorin nasa da ya sayar ba su isa ba, saboda tsadar kayan aikin asibiti.
Saboda haka ya sanya wa ’yan uwansa haraji, kowa Naira dubu 500, kuma da haka aka samu aka sayi kayan aikin asibitin.
“Na kai shekara biyu ina aikin gina wannan asibiti. Akalla na kashe sama da Naira miliyan 10 wajen gina wannan asibiti.
“Akwai wani babban likita da ya ba ni shawarar irin abubuwan da za mu saya da neman lasisi, kuma duk mun yi.
“Muna da kwararrun likitoci guda biyu da ma’aikatan jinya guda takwas kuma muna da gadajen kwantar da marasa lafiya guda 13’’, inji shi.
- Yadda ya tara kudin gina asibitin
Kawu Muhammad ya ce shi mai karamin karfi ne domin shi dan tireda ne a kofar asibitin.
Da tiredar da yake yi na tsawon shekaru ne ya samu kudaden da ya sayi kadarorin da ya sayar ya gina asibitin.
Ya ce tun suna Jos kafin su dawo NEPA da zama yake tireda.
Bayan bude asibitin an yi kwana biyu ana duba marasa lafiya tare da ba su magunguna kyauta inda aka duba sama da mutum 200.
Kawu ya ce shi ba ya bukatar komai a asibitin illa kawai asibitin ya rike kansa, saboda ba shi da karfin da zai iya rikewa.
Ya yi kira ga gwamnati ta zo ta duba asibitin, domin ta tallafa.
- An share mana hawaye –Mai unguwa
Da yake zantawa da wakilinmu, Mai Unguwar, Malam Garba Haris, ya cewa asibitin da aka gina wa al’ummar da yake shugabanta tamkar shi aka gina wa.
Ya ce da irin koke-koken da suke yi na rashin asibiti a unguwa, sun gode Allah da suka samu wannan.
Basaraken ya ce yanayin sana’ar al’ummar unguwar na harkokin manyan motoci ya sa yake da kyau a samu asibiti.
Ya kara da cewa asibitin na da saukin kudi wajen jinyar marasa lafiya, don haka ya yi kira ga al’ummar unguwar, su ba da hadin kai.
- Mazauna sun yaba
Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, wani mazaunin unguwar mai suna Isma’il Zakariya, ya bayyana farin ciki da samun asibitin.
Isma’il ya ce babu abin da za su ce wa wanda ya yi asibitin sai addu’a da fatan alheri kan wannan namijin kokari.
Tabbas asibitin da aka bude, a cewarsa, zai taimaka wa al’ummar unguwar domin babu abin da talaka yake so da ya wuce asibiti da ruwa da wutar lantarki da hanya da makaranta.