✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan takarar APC ya lashe zaben gwamnan Ekiti

Dan takarar APC Abiodun Oyebanji ya lallasa abokan hamayyarsa da gagarumin rinjaye a zaben Ekiti

Dan takarar APC, Abiodun Oyebanji, ya yi nasara a zaben gwamnan Jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar.

Mista Oyebanji ya kayar da ’yan takara 15, inda ya lashe kananan hukumomi 15 a cikin 16 na Jihar, ya kuma tashi da jimillar kuri’u 187,057.

Babban Malamin Zabe Farfesa Ayode Oyebode Adebowale ne ya sanar da hakan lokacin da ya ke bayyana kammalallen sakamakon zaben a Ado Ekiti, babban birnin Jihar.

“…A matsayina na Babban Malamin Zabe a wannan Zabe na Gwaman Jihar Ekiti na 2022 da aka gudanar ranar 18 ga watan Yunin 2022, ina tabbatar da cewa…kasancewar ya cika dukkan sharuddan da Doka ta tanada, Abiodun Obayemi Oyebanji na jam’iyyar APC  ne ya lashe wannan zabe”.

Dan takarar jam’iyyar SDP, Segun Oni, wanda ya zo na biyu, ya samu kuri’a 82,211 amma bai samu ko da karamar hukuma daya ba.

Mista Oni, wanda ya taba zama a kujerar gwamnan Jihar ta Ekiti, yana gaban dan takarar jam’iyyar PDP, Bisi Kolawole, wanda da kyar ya tashi da karamar hukuma daya da kuri’a 67,457.

‘Abin kunya…’

Sai dai kuma jam’iyyar SDP ta yi fatali da sakamakon, tana cewa za ta zarce Kotun Sauraron Korafe-korafen Zabe.

Wakilinta a wurin bayyana sakamakon, Barista Owoseni Ajayi, wanda ya bayyana haka, ya kwatanta zaben da “abin kunya”.

“Wannan zabe abin kunya ne ga Najeriya duba da yadda APC ta rika sayen kuri’un mutane a bainar jama’a.

“Wannan abin takaici ne, yadda aka rika sayen imanin mutane saboda yadda talauci ya yi katutu a Jihar – ko a zabubbukan fitar da ‘yan takarar shugaban kasa na APC da PDP mun ga haka.

“Sannan kuma da gangan wasu ‘yan barandan gwamnati suka tarwatsa zabe a wuraren da SDP ke da rinjaye – za mu tafi Kotun Sauraren Korafin Zabi, ba za mu amince da wannan ba”, inji Mista Ajayi.

Fadan Fayemi da Fayose

Ko da yake ’yan takara 16 ne suka shiga fagen daga a zaben, fafatawa ta fi zafi ne a tsakanin ’yan takarar APC da PDP da SDP.

Shi dai Abiodun Oyebanji na APC yana samun goyon bayan Gwamna mai ci, Kayode Fayemi.

Hakan ne ma ya sa ake ganin fafatawarsa da dan takarar PDP, Bisi Kolawole, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Ayo Fayose, ci gaban gwajin kwanjin da aka dade ana yi ne tsakanin Fayemi da Fayose.

Kafin zamansa dan takarar APC dai, Mista Oyebanji, wanda ya taba zama kwamishina har sau biyu, ya yi wa Fayemi Sakataren Gwamnatin Jihar.

’Yan kallo lafiya…

Galibi dai an gudanar da zaben lami lafiya, sai dai dan abin da ba a rasa ba.

Misali, akwai rumfar zaben da aka bayar da rahoton ’yan daba sun fasa akwatin zabe, yayin da a wata kuma aka ce an sace akwati.

Wani lamari da ya daga wa masu sa-ido hankali sosai shi ne batun cinikin kuri’a, inda a wurare da dama aka ce an raba kudi ko kayan abinci.

An ma bayar da rahoton cewa jami’an Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kama wadansu daga cikin mutnen da ke sayen kuri’un.