✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan takarar APC ya lashe zaben cike gurbi a Kaduna

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben cike gurbin da aka gudanar ranar Asabar na Majalisar Wakilai a mazabar Lere da ke Jihar Kaduna, Injiniya Ahmed…

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben cike gurbin da aka gudanar ranar Asabar na Majalisar Wakilai a mazabar Lere da ke Jihar Kaduna, Injiniya Ahmed Manur ya lashe zaben.

Da yake bayyana sakamakon zaben, babban jami’in da ya jagoranci, tattara sakamakon zaben, Farfesa Adamu Wada, ya dan takarar ya sami kuri’u 34,958 a yayain da Barista Ibrahim Usman, na jam’iyyar PDP, ya sami kuru’u 16,271.

Ya ce don haka a bisa doka, Injiniya Ahmed na jam’iyyar APC ne, ya sami nasarar lashe zaben.

Da yake jawabi bayan bayyana sakamakon zaben, dan takarar ya yi godiya ga Allah kan wannan nasara da ya samu.

Ya mika godiyarsa ga dukkan shugabanni, da sauran al’ummar wannan mazaba, kan gudunmawar da suka bayar, wajen ganin ya sami wannan nasara.

‘’Ina mai bada tabbacin cewa zan yi iyakar kokarina, wajen ganin na hada kan al’ummar wannan wannan mazaba. Kuma zan je wannan majalisa da manufofin bunkasa mazabar da kasa baki daya’’.

Shi ma da yake zantawa da ’yan jaridar, kan zaben, wakilin jam’iyyar PDP a wajen tattara sakamakon, Malam Yusuf A. Saminaka ya ce babu shakka an basu yawan kuri’un da aka jefa masu a wajen bayyana sakamakon zaben.

Sai dai ya koka kan yadda ya ce an debo jami’an tsaro daga wurare daban-daban aka cika mazabar a lokacin zaben.