✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan takarar APC ya ci zaben Gwamnan Sakkwato

Ahmad Aliyu Sokoto daga APC, jam'iyyar adawa a Jihar Sakkwato, ne ya zama zababben gwamna

Jam’iyyar APC ta doke jam’iyyar PDP mai mulkin Jihar Sakkwato a zaben gwamnan jihar.

Baturen Zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar Sakkwato, Farfesa Armiya’u Hamisu, ya sanar cewa dan takarar APC, Ahmad Aliyu Sokoto, ya yi nasara ne da kuri’a 453,661.

Babban abokin hamayyarsa daga Jam’iyar PDP Malam Sa’idu Umar Ubandoma, ya zo na biyu da kuri’a 404,632.

Farfesa Armaya’u wanda shi ne Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Dutinma, ya kara da cewa, Ahmad Aliyu ya cika sharuddan da aka gidanya na dokokin zabe, don haka shi ne zababben Gwamnan Jiha Sakkwato.