✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takara ya yi martani ga zanga-zangar kin sa a Kano

Sakamakon wata zanga-zangar nuna rashin amince wa da wanda jam’iyyar APC ta tsayar takarar kujerar Shugabancin Karamar Hukumar Nassarawa a jihar Kano, Hon. Auwalu Lawan…

Sakamakon wata zanga-zangar nuna rashin amince wa da wanda jam’iyyar APC ta tsayar takarar kujerar Shugabancin Karamar Hukumar Nassarawa a jihar Kano, Hon. Auwalu Lawan Aranposu, Aminiya ta tuntunbi dan takarar don jin ta bakinsa.

A zantawar da Aminiya ta yi da Honarabul Aranposu, ya ce nasarar da ya samu a yanzu Allah ne ya ba shi domin kuwa komai sai da kaddarawar Ubangiji ya ke tabbata.

A cewarsa, “Ina mai sanar muku cewa, jam’iyyar tana da matakai da take amfani da su wajen fitar da kowane dan takara kuma a kowane mataki.

“Matakin farko na fitar da dan takara shine masalaha tsakanin ’yan takara da iyayen jam’iyya kuma ta wannan hanya aka bi muka samu nasara jam’iyyar ta tsayar da mu takara.”

“Idan ban manta ba haka aka bi a takarar dan Majalisarmu na Tarayya Nasiru Ali Ahmed shi ne Uban gidan wanda ake babatu a kansa kuma Gwamna ya bawa ragowar ’yan takara hakuri.”

“Ya nemi a bar nasa kuma aka bar masa takara ba tare da kowa ya fito ya nuna adawa ko yin zanga-zangar kin amince wa da masalaha da rokon da ya yi wa sauran ’yan takara su hakura su bar masa ba.”

“Ni ba na fada da kowa kuma ba ni da wani bangare da ba na mu’amala da shi don ina mai tabbatar muke cewa, galibi mutanen da suka fito zanga-zangar nuna adawa da hukuncin da jam’iyya da Iyayen jam’iyya da masu ruwa da tsaki suka yanke ba ’yan asalin Karamar Hukumar Nassarawa bane daga waje aka hayo su don su tayar da fitina,” inji Aranposu.

Daga karshe Aramposu ya yi kira da dukkan ’yan takara da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyya da su hada kai wuri guda a ciyar da Karamar Hukumar Nassarawa gaba, tare da albishir na cewa kowa zai amfana da jagorancinsu ba tare da nuna wariya ba.

Tunda farko dai wasu matasa ’yan jam’iyyar APC magoya bayan Honarabul Baba Nabegu suka fito zanga-zagar nuna adawa da dan takarar da jam’iyyar ta fitar a matsayin wanda zai tsaya mata takara a zaben Kananan Hukumomin jihar da za a gudanar a ranar 16, ga watan Janairun 2021.

Masu zaga-zangar sun fito ne a ranar Talata rike da kwalaye masu dauke da rubutun da ke nuna adawa da hukuncin da jam’iyyar ta yanke a Karamar Hukumar.

A cewar King Cash, wani daga cikin masu zanga-zangar ya ce, sam ba a yi musu adalalci ba kuma suna jiran matakin da za a dauka a kai.

Shi ma Salim Ashiru, ya bayyana matsayar su na ‘yan jam’iyya cewa, sun marawa Rabi’u Baba Nabegu baya sai kwatsam suka ji an tsayar musu wani daban.

“A yi mana adalci a matsayinmu na ’yan karamar Hukumar Nasarawa, domin mu muka san me ke damun mu don haka bamu yarda wasu su yi karfa-karfa su baiwa wanda suka ga dama ba.”

Mu mun fi so a fito a yi zaben idan rabin kuri’a mutum ya samu a bashi abunsa,” inji Salim.

Wani mai goyon bayan Hon. Aranposu mai suna Haruna Abdulwahab Gama, ya ce masu zanga-zangar suna gudanar da ita ne kawai don bata wa kansu lokaci amma Nassarawa ta dauki layi, kuma kaso 80 cikin 100 na mutanen Nassarawa Hon. Aranposu suke goyan baya a matsayin shugaba.

Matsayar da Jam’iyyar ta dauka

Jam’iyyar APC dai ta tsayar da Hon. Auwal Lawan Shu’aib (Aramposu) a matsayin dan takararta da zai kara da sauran ’yan takara daga sauran jam’iyyun Adawa a zaben kananan hukumomin jihar Kano mai zuwa.

Jam’iyyar ta fitar da dan takarar ta hanyar masalaha da aka gudanar tsakanin ’yan takara da masu ruwa da tsaki a matakin karamar hukuma da kwamatin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa da zai jagoranci masalahar a kananan hukumomin da ke kwarayar Masarautar Kano, karkashin jagorancin Malam Salihu Sagir Takai.