✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayyuka 7 da Dangote zai yi wa Jami’ar Kano da ke Wudil

Farfesa Yakasai ya ce Dangote ya yi alƙawarin taimaka wa jami’ar a fannoni bakwai.

Shugabannin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH) da ke Wudil a Jihar Kano sun ce an dawo da wutar lantarki a jami’ar a yammacin ranar Juma’ar da ta gabata, bayan tsoma bakin Gwamnatin Jihar da kuma Gidauniyar Dangote.

Wata sanarwa da ta fito daga Shugaban Jami’ar, Farfesa Musa Tukur Yakasai, ya ce, an dawo da wutar lantarkin ce “Sakamakon gaggauta tsoma bakin Gwamnatin Jihar Kano da Uban Jami’ar Alhaji Aliko Dangote ta hannun Gidauniyar Dangote wadda ta biya Naira miliyan 100 a tashin farko inda Gwamnatin Jihar Kano ta yi alƙawarin biyan sauran basussukan da ke kan jami’ar da sauran hukumomi da ma’aikatun jihar.

Farfesa Yakasai ya ce “Gidauniyar Dangote tana duba yiwuwar magance matsalar wutar lantarki a jami’ar ta hanyar samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana.”

Ya miƙa godiyar ɗaukacin ma’aikatan jami’ar kan gaggauta tsoma baki da kuma ƙoƙarin Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ta ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Dokta Abdullahi Baffa Bichi da kuma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi Dokta Yusuf Kofar Mata.

“Muna miƙa godiya ta musamman ga Uban Jami’ar kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote da kuma Darakta Janar ta Gidauniyar Dangote da ayarinta.

“Kuma ina amfani da wannan dama waje mika godiya ga ma’aikata da daliban wannan jami’a kan hakuri da nuna sanin ya kamata da suka nuna a wannan mawuyacin hali,” in ji shi.

Sai ya roƙi mazauna harabar jami’ar su saka wannan abin kirki ta wajen tallafa wa kokarin shugabannin jami’ar ta wajen yin amfani da wutar lantarkin ta hanyar da ta kamata.

Dangote zai yi wa jami’ar goma ta arziki

A wani labarin mai nasaba da wannan da Aminiya ta ruwaito, Dangote ya kuma sha alwashin yi wa jami’ar goma ta arziki domin inganta harkokinta na ilimi.

Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske a ranar Laraba kan buƙatun da suka gabatar masa bayan miƙa godiya dangane da kuɗin lantarkin da ya biya, Farfesa Yakasai ya ce attajirin ya yi alƙawarin taimaka wa jami’ar a fannoni bakwai yayin wata ziyara da suka kai masa a ofishinsa da ke Jihar Legas.

Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin ayyukan da Dangote ya ce zai ɗauki nauyin aiwatarwa sun haɗa da gina Babban Ofishin Mahukuntan Jami’ar da gina ƙarin rukuni uku na ɗakunan kwanan ɗalibai da gidaje 10 na manyan ma’aikatan jami’ar.

Sauran ayyukan sun haɗa da inganta samar da ruwan sha da kuma ɗaukar nauyin duk wata ɗawainiya da za a yi a bikin yaye ɗaliban jami’ar karo na biyar.

Farfesa Yakasai ya ce Dangote ya jaddada ƙudirin tanadar wa jami’ar wutar lantarki mai ɗorewa da kuma tanadar wa jiga-jigan jami’ar motocin sufuri.