Wani dan dan siyasa ya yi karar bokansa da malamin tsubbunsa a wajen Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) kan zargin damfararsa bayan ya fadi zaben neman takara
Jami’an EFCC sun damke boka tare da tsubbu ne bisa zargin damfarar dan dan siyasar da ba a bayyana sunansa ba Naira miliyan 24.
- Zulum ya raba tallafin Naira miliyan 172 da kayan abinci a Damboa
- Kotu ta garkame wanda ake zargi da sace wa banki N11m a Legas
Jaridar PM ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun bugi hancin dan siyasar ne cewa za su yi msihi aiki ya ci zaben takarar Dan Majalisar Dokokin Jihar Ekiti, amma ya sha kaye.
Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya ce a ranar 7 ga Yulin 2022 aka damke su a Ado-Ekiti, Jihar Ekiti, bayan an kai karar su gaban hukumar a kan abin da suka aikata.
Jami’in ya ce a lokacin da ake binciken su, bokan ya yi ikirarin ya karbi kudade daga hannun dan siyasar har ma da karin Naira 2.9 a matsayin kudin sayen shanu da raguna da sauran kayan aiki.
Da yake maida bayani, dan tsubbun ya ce, “Namu bai wuce yin addu’o’i da yanka abin yanka ba, sannan mu bar wa Allah sauran.”
Uwujaren ya ce za a gurfanar da su biyun a kotu nan ba da dadewa ba.