✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan shekara 80 ya koyi gyaran takalma a cibiyar koyon sana’o’i

Wani dattijo mai shekaru 80 mai suna Pa Bashir Adeyemo, ya karbi takardar shaidar kammala koyon aikin gyaran takalma a cibiyar koyar da sana’o’i da…

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ne nan yayin da yake mika takardar kammala koyon aikin gyaran takalma ga Pa Bashir Adeyemo, dattijo mai shekara 80. A gefen dama, shugaban Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa ne Mista Idris Lapade. A gefe kuma wani sashe ne na mata masu koyon kitso da gyaran gashi a cibiyarWani dattijo mai shekaru 80 mai suna Pa Bashir Adeyemo, ya karbi takardar shaidar kammala koyon aikin gyaran takalma a cibiyar koyar da sana’o’i da ayyuka da ke Yemetu, Aladorin a Ibadan.
Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ne ya raba takardun shaidar ga dalibai 422 da suka koyi ayyuka daban-daban, wanda karamar Hukumar Ibadan ta Arewa ta shirya domin samar da ayyukan dogaro da kai ga jama’a.
A lokacin da yake karbar takardar shaidar, Dattijo Bashir Adeyemo ya nuna farin cikinsa da wannan shiri da karamar hukumar ta fito da shi, wanda ya bayyana cewa, “zan yi amfani da kayan aikin da aka ba ni kyauta wajen bude shago da zan rika yin gyaran takalma domin dogaro da kaina.”
Cikin jawabinsa, Gwamna Ajimobi ya jinjina wa shugaban riko na karamar hukumar, Mista Idris Lapade saboda namijin kokarin da ya yi wajen farfado da wannan cibiya, wacce take cikin shirin samar da ayyuka da gwamnati ta tanadar.
Manajan kula da cibiyar, Mista Hussein Akeem ya shaida wa wakilinmu cewa, fiye da shekara 10 da kafuwar cibiyar, ta zama holoko ba ta gudanar da aikin komai, amma Mista Idris Lapade ya farfado da ita.
Ya ce daga watan Nuwamba na shekara ta 2011 da cibiyar ta fara aiki zuwa yanzu ta yaye dalibai 1,072, wadanda aka koyar da su sana’o’i daban-daban cikin watanni 3, kuma su yi wata daya na zaman jarrabawa. “Wannan ya nuna ke nan muna gudanar da bukukuwan yaye dalibai sau uku a cikin shekara daya.” inji shi.
Sana’o’in da ake koyarwa a cibiyar sun hada da wanzanci da kitso da gyaran gashin mata da gyaran takalma da dinki da dafa abinci da kafintanci da na’ura mai kwakwalwa da makamantansu, wanda karamar Hukumar Ibadan ta Arewa take daukar nauyin bayar da kayan aiki na zamani ga dukkan daliban da suka kammala koyon.