Wani yaro mai suna Murtaza Ahmadi da ke Afgahnistan ya janyo hankalin Hukumar kwallon kafa ta kasar bayan an baza hotunansa a yanar gizo yana kwallo sanye da rigar leda da ya zama suna da kuma lamba 10 da ke kwaikwayon shahararren dan kwallon Ajantina Lionel Messi.
Rahoton ya nuna yadda yaron, dan kimanin shekara 5 yake murza leda da ta yi kama da yadda shahararren dan kwallon duniya Lionel Messi yake yi.
Rahoton ya nuna yadda hotunan yaron suka ja hankalin jama’a ta yadda wadansu suka rika yada hotunansa a kafar sadarwar intanet ganin yadda karamin yaro kamarsa zama dan-ganin kashen-nin Lionel Messi na Ajantina.
Yaron, dan kimanin shekara 5 an rika baza hotonsa a yanar sadarwar Intanet ne bayan an ga yadda yake lailaya kwallo sanye da irin rigar Lionel Messi mai lamba 10 ta Ajantina.
Rahoton ya nuna hakan ne ya janyo hankalin jama’a da dama ciki har da Hukumar kwallon kafa ta Afghanistan (FA) kuma ta kuduri aniyar tuntubar Lionel Messi don ya gana da yaron a matsayin daya daga cikin masoyansa.
Mai magana da yawun Hukumar kwallon kafa ta kasar, Sayed Ali Kazemi a ranar Talatar da ta wuce ya ce tuni suka fara tuntubar Lionel Messi don ganin ya amsa gayyatar zuwa Afghanistan don ya gana da yaron. Idan kuma Messi ba zai samu damar zuwa Afghanistan ba to Hukumar ta amince ta shirya tafiya Sifen da yaron don su gana a can. Haka kuma idan Messi ya nuna ba zai iya ganawa da yaron a Sifen ba, to ya fadi kasar da yake ganin ta fi dacewa don su gana a can.
Sayed Ali Kazemi ya kara da cewa babbar makasudin da ya sa suke son Messi ya gana da yaron shi ne don su nuna wa dan kwallon irin kaunar da yaron yake masa da kuma irin baiwar iya kwallo da Allah Ya huwacewa yaron da ta yi kama da yadda Messin ke kwallo.
Hotunan Murtaza sun bazu a yanar gizo ne a lokacin da yake kwallo a filin wasan kwallon kafa na yankin Ghazni da ke Afghanistan sanye da rigar Lionel Messi mai lamba 10 da aka dinka da buhun leda.
Hakan ya janyo hankalin Hukumar kwallon kafa ta Afghanistan, inda ta kuduri aniyar hada yaron da Messi don su gana da juna don cika burin yaron na kaunar da yake yi wa shahararren dan kwallon.
Murtaza dai iyayensa talakawa ne da ke zaune a yankin Joghori a Afghanistan, rahotanni sun nuna da alama yaron zai ci abinci da wasan kwallon kafa.
dan shekara 5 ya zama dan-gani-kashe-nin Lionel Messi
Wani yaro mai suna Murtaza Ahmadi da ke Afgahnistan ya janyo hankalin Hukumar kwallon kafa ta kasar bayan an baza hotunansa a yanar gizo yana…