✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan shekara 41 ya kai iyayensa kotu kan rashin daukar nauyinsa har mutuwa

Wani marar aiki mai shekara 41 da ya kammala digirinsa a Jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya, ya kai iyayensa kotu kan yunkurinsu na dakatar da…

Wani marar aiki mai shekara 41 da ya kammala digirinsa a Jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya, ya kai iyayensa kotu kan yunkurinsu na dakatar da ci gaba da taimakonsa.

Faiz Siddikui ya nemi kotun ta tilasta wa iyayensa ci gaba da tallafa masa da kudi har karshen rayuwarsa.

Faiz ya karanci aikin lauya ne a fitacciyar jami’ar da ke kasar Birtaniya kuma ya yi ikirarin cewa ya dogara ne da mahaifiyarsa da ke zaune a birnin Dubai tare da mahaifinsa.

Yayin ganawa da manema labarai, ya bayyana kansa a matsayin wanda yake da nakasa tun yana yaro inda yake da larurar rashin lafiya don haka dakatar da daukan nauyinsa da iyayen ke kokarin yi kamar tauye hakkinsa na dan Adam ne.

Faiz wanda ya kammala karatun digirinsa a Jami’ar Oxford tun shekara 2011, yana zaune ne ba ya da aikin yi, kuma yana gidan haya ne a gidan da kudinsa ya kai Dalar Amurka miliyan 1.4 (kimanin Naira 533 da dubu 400).

Gidan hayar mallakin mahaifiyarsa ce mai suna Rakshanda mai shekara 69 da mahaifinsa mai suna Jabed mai shekara 71, a kusa da Hyde Park da ke tsakiyar birnin Landan.

Iyayen Faiz ne suke biya masa kudin da yake bukata yayin da suke biyansa alawus duk mako da ya kai Dalar Amurka 550 kimanin Naira dubu 209 da 550) inda iyayen suka yi yunkurin dakatar da daukar dawainiyarsa kuma hakan ne ya jawo takaddama.

Iyayen sun bayyana dalilinsu na janye tallafin da suke yi wa dansu, inda suka ce sun gaji da wahala da bukatar dan mara amfani, kamar yadda lauyan iyayen mai suna Justin Warshaw KC, ya sanar wa jaridar The Sun ta Birtaniya.

Wannan ba shi ne karon farkon da Faiz Siddikui ya shigar da kara a kotun ba.

A shekarar 2018 ya taba kai karar Jami’ar Oxford kan zargin ba ta tanadi da wadatattun kayan koyarwa ba wanda a cewarsa hakan ya sa bai samu shaidar kammala karatu da shaida mafi daraja ba.

Faiz Siddikui ya taba aiki a wasu kamfanonin lauyoyi a shekarar 2011, kafin ya kai karar iyayensa kotu.