✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Sarauniya ya kai wa Shekarau ziyara

A yanzu biyayya ta koma ga tsagin Shekarau.

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiya Mu’azu Magaji, wanda aka fi sani da Dan Sarauniya, ya ziyarci tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Ibrahim Shekarau bayan kwanaki biyu da wata kotu a jihar ta bayar da belinsa.

Dan Sarauniya ya ci sarka ta tsawon kwanaki a sakamakon tuhumar da ake yi masa ta bata sunan Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai a wata ziyara ta musamman da ya kai wa tsohon gwamnan jihar, Dan Sarauniya ya bayyana goyon bayansa ga tsagin jam’iyyar mai mulki a jihar wanda kuma Shekarau ke zaman jagora.

Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin ziyarar, Dan Sarauniya ya gana da Sanata Shekarau, Sha’aban Sharada, Haruna Danzago da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, lamarin da ya gudana a yayin da wutar rikicin jam’iyya da ke tsakanin tsagin Shekarau da kuma Gwamna Abdullahi Ganduje ke ci gaba da ruruwa.

A wani taron manema labarai na gaggawa da ya wakana a gidan Shekarau a ranar Lahadi, Injiniya Magaji ya ce biyayyarsa a yanzu ta koma ga tsagin Shekarau saboda nan ne bangaren da ke yi wa Jihar Kano fatan alheri.

“Allah Ya kawo mu wannan tafiya a siyasa wadda a tarihi za mu ce tana kara mana karfin gwiwa a gwagwarmayar da muka sa gaba. Mun je kotu kuma alkali ya bayar da belin mu da sharadin mu gujewa yin tsokaci kan lamarin da ya kai mu gabansa.

“Za mu yi riko da gaskiya wajen yi wa umarnin kotu biyayya saboda kasancewar mu ’yan kasa na gari.

“A yanzu ga mu a gidan jagoranmu, Shekarau wanda ya kafa sabuwar tafiya har ta kai ga mallakar ikon jamiyyar APC a Jihar Kano a siyasance da kuma mataki na sharia.

“Za mu ci gaba da fafutika kan abinda ya dace, fadin gaskiya da kuma tsayuwa kan gaskiya. Abin da za mu yi nan gaba shi ne karfafa kungiyar mu wurin samun nasarar kafa sabuwar Kano kamar yadda muka zo neman tabarraki a wurin shugabanmu.

“Burinmu a yanzu shi ne hada kan matasan Kano da kasar nan baki daya wurin samar da dama da za ta sauya tsarin shugabanci.

“Babu shakka akwai sadaukarwa kuma dole sai an fuskanci kalubale yayin sadaukarwa. Babu kuma raguwa idan har za ka tabbatar da cewa an yi komai daidai,” a cewar Dan Sarauniya.