✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan sanda ya shiga hannu kan zargin garkuwa da mutane

Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani dan sanda da ake zargi da hada baki da wadansu suna garkuwa da mutane. Sakamakon aikin hadin…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani dan sanda da ake zargi da hada baki da wadansu suna garkuwa da mutane.

Sakamakon aikin hadin gwiwa a tsakanin Rundunar ’Yan sandar Jihar da kungiyoyin Fulani ne aka yi nasarar kama mutum 71 da daya wadanda a cikinsu akwai masu garkuwa da mutane da barayi da masu fyade.

Kwamishinan ’Yan sandar Jihar, Audu Madaki ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce dan sandan da aka kama sunansa Abdulrazak Dahiru, wanda a halin yanzu ake ci gaba da bincike a kansa.

“A ranar 8 ga Maris din nan ne lokacin da muke bincikar wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane, daya daga cikinsu ya bayyana mana cewa Saje Abdulrazak Dahiru ne yake taimaka musu,” inji shi.

Ya ce Dahiru ya ba su makami domin gudanar da ayyukan ta’asarsu har sau uku kafin suka shiga hannu.

Kwamishinan ya ce sun yi nasarar samun bindigogi 13 wadanda a cikinsu akwai AK47 da harsasai 761 da bindigogin gargajiya biyar.

Kwamishinan ya jinjina wa kungiyoyin  Miyetti Allah da na Tabital-Pulaku domin ba su hadin kai da taimaka musu da sauran jami’an tsaron jihar.

Kwamshina Madaki ya ce masu garkuwa da mutane su 11 sun tuba kuma suka yi ratsuwar fallasawa da kama duk wadanda suka san yana da hannu a cikin wannan aiki.