✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan sanda ya mutu a musayar wuta da ’yan bindiga a Ebonyi

Anyanwu ya ce, lamarin wanda ya faru da misalin karfe 9:00 na dare ya lakume jami’insu daya da dan bindiga guda.

Wani dan sanda ya rasa ransa sakamakon musayar wutar da wasu bata-gari ranar Litinin a  Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi.

Bayanai sun nuna wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi arangama da ’yan sandan a bakin aiki inda aka yi musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Chris Anyanwu, ya tabbatar da faruwar hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Talata a Abakaliki.

Anyanwu ya ce, lamarin wanda ya faru da misalin karfe 9:00 na dare ya lakume jami’insu daya da dan bindiga guda.

“Haka ne. Ina da masaniyar harin da aka kai wa jami’anmu. Dan sanda daya ya mutu, haka ma dan bindiga daya,” in ji shi.