Wani dan sanda mai mukamin ASP ya yi ajalin abokin aikinsa ta hanyar daba masa almakashi a Jihar Kebbi.
Bayanai sun ce wannan abin al’ajabin ya faru ne a garin Argungu da ke jihar, bayan rashin jituwar da ta shiga tsakanin jami’an biyu.
- ’Yar haya ta sace yara kwana 3 da shigarta gida
- Kotu ta daure tsohon jami’in MDD kan yi wa mata 20 fyade
An ce wanda ake zargi da aikata kisan, shi ne jami’i mai rike da ofishin ’yan sanda na Sauwa, yayin da marigayin wanda shi ma mukamin ASP gare shi, ya kasance babban jami’i a hedkwatar ’yan sanda da ke Argungu.
A cewar PM News, tsamar da ke tsakanin jami’an biyu ta rikide ta zama fadan raba raini, inda wanda ake zargin ya zaro almakashi ya daba wa marigayin a hakarkarinsa na hagu.
Majiyarmu ta ce bayan mai aukuwa ya auku, jami’an tsaro sun ziyarci wurin da aka yi fadan inda suka kama wanda ya daba wa dan uwan nasa almakasi, sannan shi da aka yi wa rauni aka dauke shi zuwa asbiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Wannan al’amari ya faru ne a ranar 19 ga Oktoba kamar yadda bayanan mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP. Nafi’u Abubakar suka nuna.
Ya ce an mika batun ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ahmed Magaji Kontagora don zurfafa bincike.