Wani dan sanda ya bude wa surukinsa wuta ya kuma harbe wasu ’yan sandan kwantar da tarzoma shida har lahira kan sabani da iyalinsa.
Bayan bude wutar, dan sandan mai mukamin Sajan, ya kona gidaje da dama, saboda rikicin da yake da matarsa a barikin ’yan sanda da ke Kwalejin ’Yan Sanda a Maiduguri, Jihar Borno, a daren Alhamis.
- Jama’ar gari sun kona masu kwacen waya da ransu
- ISWAP za ta kai hare-haren kunar bakin wake a Najeriya —DSS
“Ya harbi surukinsa, sannan ya kona jerin gidaje hudu, kowannensu iyalai takwas ne a ciki.”
Wani makwabcinsa ya ce tun lokacin da ma’auratan suka samu matsala makwabta suka yi ta kokarin sasanta su amma mutumin ya ki.
“A sanadiyyar kwashe kayan da ta yi saboda yadda ta ce yana musguna mata ne ya bude wa mutane wuta ranar Laraba da dare.”
Wani babban dan sanda a barikin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.
Ya ce, “Suna yawan rikici da matarsa, mu da matan wasu manyan hafsoshinmu mun sha kokarin sasanta su, mun sha yi mishi magana, ba ya ji.”
Ya bayyana cewa bayan matar ta kwashe kayanta ne mijin ya sha alwashin sai ya kashe mutane, idan har ba ta dawo ba.
Ya ce daga baya an yi nasarar tsare dan sandan, bayan da ya yi aika-aikan.
Aminiya ta gano cewa a halin yanzu Sajan din yana tsare a Sashen Binciken Manyan Laifuka a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Borno.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske daga hukumomin ’yan sandan jihar, amma abin ya faskara.