Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta tabbatar da wani jami’inta ya harbi wani direban babbar mota a kan hanyar Gombe zuwa Kano, saboda ‘na goro’.
Ana zargin jami’in mai suna Urbanus Ishaya, mai mukamin sufeta wanda ke aiki da sashen kwantar da tarzoma wato mobile PMF 34 da ke Jihar, da harbin direban mai suna Abdullahi Bello.
- Sojoji sun kara kashe masu zanga-zanga 7 a Sudan
- Ayyukan ta’addanci ba za su kare a nan kusa ba – Gwamnan Zamfara
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ishola Babatunde Babaita, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a Jihar ranar Litinin.
Sanarwar, wacce ke dauke da sanya hannun jami’ar hulda da jama’a ta rundunar, SP Mary Malum, ta ce yanzu haka dan sandan yana hannu yana fuskantar bincike a sashen kula da manyan laifuka na rundunar.
Shi ma da yake zantawa da manema labarai a Gombe, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar a madadin gwamnati, Mista Julius Ishaya, ya ce dan sandan ya harbi direban ne a kwanar shiga garin Hashidu, inda sauran direbobin manyan motar da suka ga haka suka tare hanyar Gombe zuwa Kano.
Ya ce direban bai mutu ba, amma yana kwance a Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Gombe inda yake karbar magani, kuma gwamnati ce ta dauki nauyin kudin jinyarsa.
A cewar Kwamishinan, shiga tsakanin da gwamnati ta yi ya kawo sauki inda tuni direbobin da suka tare hanyar suka budeta aka ci gaba da zirga-zirga.
Da wakilinmu ya tuntubi Shugaban Kungiyar Direbobin Manyan Motocin Dakon Kaya, Mohammad Muhammad, ya ce ya zanta da direban inda suka shaida masa cewa lamarin ya faru ne a shingen ’yan sandan.
Ya ce da yake lokacin dare ya yi, sai ya kwana a wajen, inda da safe shi dan sandan sai ya nemi ya ba shi na goro kafin ya wuce sai direban ya ki, inda a nan ne dan sanda ya yi harbi sama sau daya na biyu sai ya dirka masa harsashin.