Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta yi tir da abin da ake zargin wani jami’inta da aikatawa na kashe farar hula da jikkata wadansu mutum uku.
Kakakin Rundunar, ASP Muhammad Abubakar Sadik ne ya fitar da bayanin hakan yayin zantawa da manema labarai.
ASP Muhammad ya ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan kammala addu’a ta musamman kan cikar Najeriya shekara 60 a Masallacin Juma’a na Sultan Bello da ke Fadar Sarkin Musulmi.
“Bayan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da kyautar kudi ga mabukata, a wajen rabon ne kasancewar akwai yawan jama’a Sajan Bello Garba daga Sashen Kwantar da Tarzoma na 18 da ke Gusau, da da ke aiki a Gidan Gwamnatin Sakkwato, ya yi harbi da bindiga, ya yi sanadiyar kashe Abdurrahman Aminu mai shekara 25.
“Junaidu Abba da Babangida Muhammad da Awaisu Alti kuma suka samu raunuka.
Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya bayar da umarnin tsare jam’in tare da gudanar da bincike kan lamarin.
“Gwamna Aminu Tambuwal ya je gidansu mamacin don yi musu ta’aziya tare da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ibrahim Ka’oje, inda ya yi alkawarin za a hukunta wanda aka samu da laifin kisan”, inji sanarwar.
Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne lokacin da matasan ke rabo, inda suka fara fada a tsakaninsu dauke da makamai, suna sarar juna, “Ganin haka ne sai dan sandan ya yi harbi, inda ya kashe Abdurrhaman Aminu wanda ake kira Banna sannan harsashin ya jikkata wadansu mutum uku.
“A zatona dan sandan don yana bako ne ya yi harbin, domin matasan suna fada da junansu lokaci-lokaci har su jikkata juna in sabani ya shigo tsakaninsu.
“Mutum ukun da aka kai asibiti an sallami biyu saura daya yana jinya”, inji shi.