✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan sanda ya harbe lauya ranar Kirsimeti a Legas

Tuni aka tsare dan sandan da ya yi harbin kuma ana fadada bincike a kai

An kama wani dan sanda mai mukamin ASP bisa zarginsa da kisan wata lauya kuma mai harkar gidaje, Bolanle Raheem, a ranar Kirsimeti a Jihar Legas.

A yayin da lamarin ya faru dai, dan sandan na tare da wasu abokan aikinsa su biyu a unguwar Ajah da ke Jihar Legas, kuma tuni aka kulle shi.

Bayanai sun nuna cewa Bolanle na tare da ’yar uwarta da ’ya’yanta su hudu, lokacin da suke kokarin ficewa daga wani wajen cin abinci, a lokacin da dan sandan ya bindige ta a karkashin gadar Ajah.

Rahotanni sun ce Dan sandan ya harbi wata mota ce da ke tafiya, inda harsashin ya same ta. An ce ta rasu a asibiti ne bayan an garzaya da ita.

Wani mai amfani da shafin Twitter mai suna “Speak it forth,” ya yi korafin cewa dan sandan wanda ke aiki da ofishin Ajiwe, ya yi kaurin suna wajen azabtar da mutane.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce tuni suka far bincike kan lamarin.

“Abin da ya faru abin takaici ne wanda za a iya kauce masa. Tuni mun tsare dan sandan da ya yi harbin tare da wadanda ke tare da shi a lokacin.

“Yanzu haka an mayar da su Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar domin zurfafa bincike a kan lamarin,” inji Kakakin.