An kaddamar da bincike bayan ’yan sanda sun bude wa wasu sojoji wuta, suka kashe daya, a yayin da daya kuma ya sha da kyar da munanan raunuka.
Lamarin da ya haifar da zaman dar-dar a tsakanin jama’a ya faru ne a yankin Nakuse da ke Karamar Hukumar Toto da Jihar Nasarawa a ranar 5 ga watan Maris din da ya gabata, kamar yadda Aminiya ta gano.
- Aisha Buhari ta gayyaci ’yan takarar shugaban kasa liyafar bude baki
- Yadda Boko Haram ta yi wa mutum 11 yankan rago a Geidam
Da yake tabbbatar da hakan, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce, “Wajibi ne a sani cewa gwamnati ba za ta yi sakaci wajen daukar matakin kan abin da ya faru a Nakuse ba, amma tun da hukumomin tsaro na daukar mataki a kai, ya sa muka jira mu ga fitowar sakamakon.”
Ya bayyana haka ne a gidan gwamnatin jihar, lokacin da yake rantsar kwamitin binciken da ya kafa domin gano hakikanin abin da ya faru domin daukar matakin da kuma hana maimaituwar irin hakan.
Gwamnan ya ce, saboda muhimmancin tabbatar da hadin kai da kuma yin aiki kafa-da-kafada a tsakanin hukumomin tsaro, “Mun zabo mashahurin masanin shari’a da kwararrun masana a harkar tsaro da na gudanarwa da sauransu, muka nada su a wannan muhimmin kwamitin bincike.”
Ya ce aikin kwamitin wanda zai gabatar da rahotonsa bayan mako uku shi ne gano ainihin musabbabin abin da ya faru da kuma masu hannu a cikinsa.
Kwamitin zai kuma ayyana mai laifi da hukuncin da za a yi mishi da kuma diyyar da za a biya iyalan sojan da aka kashe da kuma wanda aka ji wa rauni.
Ana kuma bukatar kwamitin ya bayar da shawarwari kan yadda za a kauce wa maimaituwar irin haka da ma sauran abubuwan da suka danganci hakan.
Kwamitin dai zai kasance ne a karkashin jagorancin tsohon Babban Alkalin Jihar Nasarawa, Mai Shari’a Badamasi Maina.