✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan sanda ya bindige ma’aikaciyar otel a Yobe …Wanda ya harbi abokan aikinsa ya gurfana a kotu a Kano

Wani dan sanda mai mukamin kofur da ke aiki a sashin binciken manyan laifuffuka a Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe ya bindige wata ma’aikaciyar wani…

Wani dan sanda mai mukamin kofur da ke aiki a sashin binciken manyan laifuffuka a Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe ya bindige wata ma’aikaciyar wani otal a Damaturu.
Wani abokin aikin matar da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar wa Aminiya cewa, kofur din ne ya harbe abokiyar aikinsa mai suna Rebecca Dabid kuma ba su san dalilin harbin ba, saboda ba su ji wata hatsaniya ta tashi a tsakaninsu ba.
Ya ce da ya ji karar harbin ne sai ya rugo ya ga abokiyar aikinsa a kwance tana shure-shure a yayin da jini ke zuba ba kakkautawa a kanta saboda a kai ya harbe ta.   
Ma’aikacin ya kara da cewa sun gaggauta sanar da jami’an tsaro inda nan take jami’an tsaron tare da shi wanda ake zargin suka dauki marigayiyar zuwa Asibitin Sani Abacha. Wata majiya a asibitin na Damaturu ta ce marigayiya Rebecca da aka kai ta da misalin karfe 8.30 na yamma ta riga ta rasu kafin kai ta asibitin, kuma a kai aka harbe ta.
Kakakin ’yan sandan Jihar Yobe Mista Nansak Chegwa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, kofur din da ba a bayyana sunansa ba yana aiki ne a sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar kuma bai yi tsammani kofur din ya harbi marigayiya Rebecca da niyya ba, amma bincike ne zai tabbatar da gaskiyar lamarin. Ya ce sun kama jami’in nasu don bincikar wannan aika-aika matukar kuma an tabbatar da gagganci ne, zai fuskanci hukuncin da ya dace.
A wani labarin kuma wani kofur din ’yan sanda mai suna Rabi’u Usman ya gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kano ta 16 da ke Titin Miller a yankin Bompai, bisa zarginsa da harbin abokan aikinsa a ofishin shiyya na ’yan sanda da ke Tsanyawa a jihar a ranar 25 ga Nuwamban 2012.
A yayin da ake karanto tuhumar da ake yi wa wanda ake zargin, a zaman kotun na ranar 1 ga watan Yuli na 2014, an bayyana mata cewa dan sandan ya yi amfani da bindiga kirar AK-47 wajen harbin Sufeton ’yan sanda Muhammad Musa, inda harsashin ya goge shi a ciki, kuma ya bude wuta da bindigar a kan wani kurtun dan sanda, mai suna Sani Daura ya kuskure shi, bai same shi ba.
Wanda ake zargin ya bayyana a gaban kotun, sai dai ba a ba shi damar magana don amsawa ko musanta tuhumar ba, sai zuwa zaman kotun na gaba.
Mai shari’a Amina Aliyu Adamu ta ce laifin da ake tuhumar dan sandan ya saba wa sashi na 95 na kundin manyan laifuffuka.