✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Sanda Ya Bindige Direba Kan N200

Wani dan shekara 40 da ‘ya’ya uku mai sana’ar kabu-kabu a cikin gari ya gamu da ajalinsa saboda ya hana ’yan sanda cin hancin Naira…

Wani dan shekara 40 da ‘ya’ya uku mai sana’ar kabu-kabu a cikin gari ya gamu da ajalinsa saboda ya hana ’yan sanda cin hancin Naira 200. 

Dan sanda ya harbe direban ne a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Mummunan al’amarin ya faru ne a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu a kan hanyar Azikoro a cikin Yenagoa, da misalin karfe 8 na dare.

Lamarin ya janyo tofin Allah tsine daga jama’ar yankin da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama.

Rahotanni daga jihar Bayelsa na cewa har yanzu rundunar ’yan sandan jihar ba ta bayyana sunan jami’in da ya aika laifin ba.

cewa marigayin dan asalin kauyen Ayakoromo Bobougbene a Karamar Hukumar Burutu ne da ke zaune Yenagoa.

An ce, dan sandan ya bindige direban a cikin motarsa kirar Sienna ne yayin da yake dauke da fasinja daya a kujerar gaba.

Wasu mazauna unguwar da suka shaida faruwar lamarin sun ce,  ’yan sandan da ke sintiri a kan titin sun tsayar da shi domin ya ba su Naira 200, kamar yadda suka saba karba a hannun masu ababen hawa.

Marigayin ya ce ba shi da shi a halin yanzu, nan take ’yar gardama ta shiga tsakaninsu, sai dan sandan ya saita shi ya bindige shi.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Bayelsa, ASP Musa Muhammed, ya ce nan gaba zai fitar da sanarwa kan lamarin.