✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Najeriya ya fi kowane dan kwallo tsada a kulob din Watford

Wani dan kwallon Najeriya mai suna Isaac Succes ya fi kowane dan wasa tsada a kungiyar kwallon kafa ta Watford da ke kasar Ingila.dan wasan…

Wani dan kwallon Najeriya mai suna Isaac Succes ya fi kowane dan wasa tsada a kungiyar kwallon kafa ta Watford da ke kasar Ingila.
dan wasan wanda ya sa hannu a kwantiragi na shekara biyar a kan Fam miliyan 12 da rabi hakan ya sa ya zama dan kwallon mafi tsada a tarihin kungiyar ta Watford.
Success wanda ya buga wasanni 30 a kungiyar Granada a rukunin La Liga da ke kasar Spain a kakar wasa da ta gabata ya zura kwallaye shida kokarinsa a wasa ya sa aka ba shi dan kwallon shekara na kungiyar Granada.
kungiyar kwallon kafa ta Watford ta tabbatar da sayen dan wasan a shafinta na twitter inda ta ce, “kungiyar Watford tana farin cikin sanar da sayen dan wasan gaba Isaac Succes a kudi mafi tsada a tarihin kungiyar.”
Mai shekara 20, Isaac Succes shi ne na uku da kungiyar ta saya bayan da Walter Mazarri ya zama sabon mai horar da kungiyar.