Wani matashi dan damben boksin dan asalin Najeriya Rilwan Oladosu ya zama zakara a gasar damben boksin ta GOtb karo na 17 a Jihar Legas, inda ya samu kyautar Naira miliyan 3. Baya ga kyautar, an kuma hada masa da kofin “Mojisola Ogunsanya Memorial Trophy.”
Gasar wacce Kamfanin GOtb ke shiryawa duk shekara, an gudanar da ta bana karo na 17 a Legas ce ranar Juma’ar da ta wuce a yayin bikin Kirsimeti da kuma murnar sabuwar shekarar bana.
Rilwan wanda ake wa lakabi da “Real One” ya doke abokin kawarwarsa Mubarak Hamzat dan asalin Maroko tun a zagayen farko a ajin marasa nauyi.
Kamfanin GOtb yana gayyato ’yan wasan boksin ne daga sassan Afirka da suka hada da Maroko da Tanzaniya da Ghana da sauransu.
A wani damben kuma, ’yan Najeriya biyu Oluwafemi Oyeleye da Seun Wahab ne suka samu nasarar doke abokan karawarsu ’yan asalin Ghana da Tanzaniya duk a gasar da Kamfanin GOtb ya dauki nauyi.
A hirarsa da mamena labarai Rilwan ya nuna farin cikinsa game da wannan nasara da ya samu, kuma yana fatan zai ci gaba da kokari a gasannin damben da za a shirya a ciki da wajen Afirka.
Dubban jama’a ne suka kashe kwarkwatar idanu a lokacin da gasar ta gudana, kuma da dama sun yaba wa Kamfanin GOtb game da daukar nauyin gasar damben boksin din.